Fargaba: jiga-jigan APC da ministocin Buhari sun fara ganawar sirri da Atiku

Fargaba: jiga-jigan APC da ministocin Buhari sun fara ganawar sirri da Atiku

- Majiya da dama daga cikin jam’iyyar PDP sun bayyana cewar wasu jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar APC sun yi ganawar sirri da Atiku

- A cewar su, manyan ‘ya’yan jam’iyyar ta APC sun gana da Atiku ne bisa fargabar cewar zai iya lashe zaben da za a yi ranar Asabar

- Sai dai, Paul Ibe, kakakin Atiku, ya ki cewa komai a kan sahihancin labarin ganawar ta Atiku da jiga-jigan jam’iyyar APC

Wasu majiya da dama daga cikin jam’iyyar PDP sun bayyana cewar wasu jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar APC sun yi ganawar sirri da Atiku Abubakar bias fargabar cewar tsohon mataimakin shugaban kasar zai iya lashe zaben da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

A cewar su, manyan ‘ya’yan jam’iyyar ta APC sun gana da Atiku ne domin kulla yadda za a yi tafiya da su idan ya kafa gwamnati.

Yanzu yayin Atiku ake yi kuma hakan da su ka yi ya nuna cewar sun a da wayewa irin ta siyasa, musamman ganin cewar babu masoyi ko makiyi na dun-dun-dun a tafiyar siyasa,” kamar yadda daya daga cikin majiyar ya fada.

Fargaba: jiga-jigan APC da ministocin Buhari sun fara ganawar sirri da Atiku

Atiku da wasu jiga-jigan APC
Source: Facebook

Daga cikin wadanda su ka gana da Atiku akwai wasu manyan ministocin gwamnatin Buhari guda biyu, kamar yadda wata majiya da ba ta yarda a ambaci sunan ta ba ta tabbar.

DUBA WANNAN: Jayayya da jam'iyya a kan Buhari: SDP ta kori dan takarar ta na shugaban kasa

Kazalika, ana rade-radin cewar akwai wani babban dan siyasa daga jihar Legas da ke tattauna wa da Atiku domin ganin yiwuwar yadda zai yi ma sa aiki a sirrance a zaben shugaban kasa na ranar Asabar.

Majiyar ta kara da cewa mai yiwuwa mutanen uku su yi wa Atiku aiki lokacin zabe idan sun kai ga cimma kulla yarjejeniya kafin lokacin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel