Mun kama Ben Bako ne saboda kalamansa na tunzura jama'a - Hukumar DSS

Mun kama Ben Bako ne saboda kalamansa na tunzura jama'a - Hukumar DSS

- Hukumar DSS reshen jihar Kaduna tace tayi nasarar cafke shugaban PDP sakamakon kalaman shi

- Hukumar tace bazata yi kasa a guiwa ba wajen bincikar shi don kada ya kasance barazana ga jama'ar jihar

- Hukumar tayi alkawarin hada kai da cibiyoyin tsaro wajen ganin yanci ya samu ga 'yan jihar

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Source: UGC

Hukumar DSS reshen jihar Kaduna sun ce sun cafke shugaban yakin neman zaben PDP, Ben Bako, akan kalaman shi.

Shugaban kamfen din PDPn an kama shi ne bayan faifan bidiyon da ya saki inda yake cewa duk wanda yaki zabar PDP a zabe mai zuwa a kashe shi.

Hakan ya biyo bayan ikirarin da jam'iyyar PDP tayi na cewa an kama shi ne saboda durkusar da babbar jam'iyyar adawa.

Hukumar DSS, a takardar da suka fitar a ranar talata a Kaduna wacce shugaban hukumar na reshen jihar Kaduna, AI Koya, yasa hannu, yace in aka bar shugaban na PDP, zai iya kawo nakasa ga dokar jihar da ma kasar.

Takardar ta cigaba da sanarwa cewa an kama Bako ne don ya kara bayani akan maganar shi gani da cewa mutanen da suke magana yanayin wannan ana kara bincike akan su kuma suna fuskantar fushin hukuma kamar haka.

Takardar tace, "A ranar 9 ga watan Fabrairu, wannan hukumar ta gayyaci Mr. Ben Bako da ya kara bayani akan maganar shi da yake kira da hargitsi a jihar. A ranar 7 ga wata Mr Bako ya yi ma yan kamfen jawabi a Kafanchan, karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna. Yayi kira ga mabiyan shi akan su kashe duk wanda ya zabi wata jam'iyyar da ba PDP ba. A halin yanzu faifan bidiyon ya watsu a kafafen sada zumunta."

GA WANNAN: Boko Haram: Yankin mazaba ta yanzu babu matsalar tsaro - Sanata Binta ta Adamawa

"Bako, tsohon kwamishinan yada labarai a jihar kuma shugaba yayi kira ga magoya bayan shi a Kafanchan akan su halaka duk wanda ya zabi wata jam'iyyar da ba PDP ba. Wannan ganganci ne da zai iya tada hargitsi a jihar. Idan aka bar wannan cigaban ba tare da bincike ba, zai iya kawo nakasa a dokar jihar ko fiye da hakan,"

"A halin yanzu, ana binciken Bako a hukumar kuma za a gurfanar dashi gaban kuliya ana kammala binciken."

"Hukumar nan na tabbatarwa da jama'ar jihar Kaduna cewa zata hada kai da cibiyoyin tsaro don tabbbatar da yan jihar sun samu yancin zamantakewa da zabin kansu ba tare da shamaki ba."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel