An damke sojin bogi 4 a jihar Imo masu raka yan siyasa

An damke sojin bogi 4 a jihar Imo masu raka yan siyasa

Gabanin zaben shugaban kasa da yan majalisar dokokin tarayya da zai gudana ranan Asabar, jami'an tsaro a jihar Imo sun damke wasu sojin bogi hudu wadanda aikinsu raka yan siyasa duk inda zasu je domin aika-aika.

Kwamishanan yan sandan jihar Imo, Dasuki Galadanci, wanda ya bayyana sojin bogin a garin Owerri ya nuna bacin ransa musamman yayinda zaben kasa ya gabato.

Galadanci ya kara da cewa sai sun kama masu iri wannan hali duk irin basarwa da sukayi. Kana ya yi kira ga yan siyasa su bi doka kuma kada su tayar da hankali.

Yace: "Za ku yarda da ni cewa irin wannan zaman lafiya da muke samu a jihar Imo abune wanda ya kamata mu yiwa rikon kwai, wajibi ne mu cigaba a kan a yanzu da bayan zabe."

Kwamandan 34 Artilari Obinze, Birgediya Jaar H. I Bature, ya gargadi masu aikata irin wadannan abubuwa cewa ko suna cakude cikin sojoji dari biyu, sojoji sun san yadda zasu gane na kwarai.

Ya ce hukumar soji zata kasance cikin farga lokacin zaben nan tunda sojin bogi sun fara shirin tayar da hankali da zabe.

KU KARANTA: Zaben 2019: Kungiyar yan darikar Tijjaniyya ta umurci mabiyanta su zabi Buhari

A shekaru biyu da suka gabata, Rundunar Sojin ruwa ta yi ma wasu Sojojin gona diran mikiya yayin da suke gudanar da atisaye a garin Opokgu dake jihar Benuwe, kamar yadda Legit.ng ta jiyo.

Wadannan Sojin bogi masu suna ‘Costal Defence Force, 4th Arms Signal Ship Base operating’, wato Sojojin ruwa na musamman, kamar yadda suka bayyana kansu, suna zambatar samari ne da nufin shigar dasu aikin Soji.

Sai dai jami’an Sojin ruwan Najeriya sun samu rahoton ayyukan matasan, inda suka kai samame a sansanin su, suka kuma samu sa’ar kama katta 24 da shekarunsu bai gaza 24 ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel