Yanzu Yanzu: Kungiyar ACF ta goyi bayan takarar Buhari

Yanzu Yanzu: Kungiyar ACF ta goyi bayan takarar Buhari

- Kungiyar Arewa Consultative Forum ta tsayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takaranta a zabe mai zuwa

- Kungiyar tace tana sane da cewa fitattun yan arewa biyu suna yunkurin neman shugabancin kasa, Wanda hakan ne yasa kungiyan ta binciki ayyuka da nasarori da kowannensu ya samu a baya

- ACF ta kuma ce ta lura da nasarori da gwamnatin Buhari ta samu wajen inganta tattalin arzikin kasar tare da nasaran da aka samu wajen yaki da ta’addanci

Kungiyar Arewa Consultative Forum ta tsayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takaranta a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Mukaddashin shugaban kungiyar ACF na kasa, Alhaji Musa Usman Kwande, wanda yayi magana a madadin kungiyar yace kungiyar tana sane da cewa fitattun yan arewa biyu suna yunkurin neman shugabancin kasa, Wanda hakan ne yasa kungiyan ta binciki ayyuka da nasarori da kowannensu ya samu a baya kafin ta yanke shawara.

Yanzu Yanzu: Kungiyar ACF ta goyi bayan takarar Buhari

Yanzu Yanzu: Kungiyar ACF ta goyi bayan takarar Buhari
Source: Facebook

Yace kungiyan ACF ta lura da nasarori da gwamnatin Buhari ta samu wajen inganta tattalin arzikin kasar tare da nasaran da aka samu wajen yaki da ta’addanci.

KU KARANTA KUMA: Zolaya Buhari ke yi cewa da yayi kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi – Kwamitin Kamfen

Ya bayyana cewa, “a yunkurin gwamnatin wajen taimakawa tattalin arziki da kayan more rayuwa tare da cigaba da aka samu a fannin yaki da ta’addanci da harkar tsaro da kasar ke fuskanta, Kungiyar ACF ta yarda da yunkurin sake tsayawa takaran shugaban kasa Muhammadu Buhari a Karo na biyu”

Kungiyar ACF tayi kira ga yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani tashin hankali kafin zabe da kuma bayan zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel