Cunkuso: Mutane 4 sun mutu a wurin kamfen din APC a jihar Ribas

Cunkuso: Mutane 4 sun mutu a wurin kamfen din APC a jihar Ribas

- Mutane hudu sun mutu a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu a wajen gangamin kamfen din shugaban kasa na jam’iyyar APC wanda aka gudanar a Port Harcourt, jihar Ribas

- Sun mutu ne sakamakon yawan cunkoso da aka samu wajen fita daga filin wasa na Adoki Amasieme

Mutane hudu sun mutu a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu a wajen gangamin kamfen din shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda aka gudanar a Port Harcourt, jihar Ribas.

Wasu yan tsiraru kuma sun jirauni daban-daban sannan an kwashe su zuwa asibiti domin samun kulawa, kamar yadda wakilinmu ya samu labari.

Cunkuso: Mutane 4 sun mutu a wurin kamfen din APC a jihar Ribas

Cunkuso: Mutane 4 sun mutu a wurin kamfen din APC a jihar Ribas
Source: Depositphotos

Wani idon shaida ya bayyana cewa an garkame mutanen ne a kofar fita daga filin wasa na Adoki Amasieme yayinda suke kokarin fita daga filin.

A wani lamari makamancin haka, mun ji cewa wasu yan iska sunyi yunkurin hargitsa yakin neman zabe da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke gudanarwa a filin Tafawa Balewa (TBS) da ke jihar Lagas.

KU KARANTA KUMA: Zolaya Buhari ke yi cewa da yayi kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi – Kwamitin Kamfen

Rikici ya barke ne tsakanin wasu matasa kusa da aihanin munbarin da shuwagabanin jam’iyya ke zaune. Lamarin, Wanda ya faru misalin karfe 1:50 na Rana, ya hada da jefe jefen kujeru da kuma fadace-fadace.

Ba a gano mussababin faruwa rikcin ba. Wadanda ke a haraban sun tsere, yayinda yan sanda suka kore yan iskan daga wajen.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel