Jayayya da jam'iyya a kan Buhari: SDP ta kori dan takarar ta na shugaban kasa

Jayayya da jam'iyya a kan Buhari: SDP ta kori dan takarar ta na shugaban kasa

Jam’iyyar SDP mai alamar doki ta dakatar da Donald Duke, dan takarar ta na shugaban kasa bias zargin sa da cin dunduniyar jam’iyya.

Jam’iyyar SDP mai fama rikici a tsakanin ‘yan takarar ta na shugaban kasa; Donald Duke da Jerry Gana, ta yanke shawarar goyon bayan shugaba Buhari a zaben da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

Wannan mataki da jam’iyyar ta dauka bai yi wa ‘yan takarar biyu dadi ba, lamarin da ya sa su ka yi fatali da umarnin jam’iyyar na neman dukkan mambobin ta su goyi bayan Buhari.

Yemi Akinbode, darektan yada labarai na jam’iyyar SDP, ne ya bayar da sanarwar matakin da jam’iyyar ta dauka a kan Donal Duke da Jerry Gana bayan kamala wani taro a Abuja.

Jayayya da jam'iyya a kan Buhari: SDP ta kori dan takarar ta na shugaban kasa

Duke da Gana
Source: Twitter

Akinbode y ace jam’iyyar ta kori Jerry Gana tare da dakatar da Donald Duke bias nuna rashin da’a da cin dunduniyar jam’iyyar SDP.

DUBA WANNAN: Zabe: AD, MAAN, NAC da NHRC sun goyi bayan Buhari

An kori Jerry Gana ne saboda kawo cikasa a lamuran jam’iyya yayin da aka dakatar da Donald Duke saboda nuna raini ga jam’iyya.

SDP ta zargi Jerry Gana da kafa shugabancin jam’iyya na kashin kan sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel