Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin PDP a Lagas inda yan daba ke ta jifan junansu da kujeru

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin PDP a Lagas inda yan daba ke ta jifan junansu da kujeru

- Wasu yan iska sunyi yunkurin hargitsa gangamin kamfen din jam'iyyar PDP a Lagas

- Rikici ya barke ne tsakanin wasu matasa kusa da aihanin munbarin da shuwagabanin jam’iyya ke zaune

- Sai dai ba gano mussabbabin rikicin ba wanda ya haddasa jefe-jefe a tsakanin matasan

Wasu yan iska sunyi yunkurin hargitsa yakin neman zabe da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke gudanarwa a filin Tafawa Balewa (TBS) da ke jihar Lagas.

Rikici ya barke ne tsakanin wasu matasa kusa da aihanin munbarin da shuwagabanin jam’iyya ke zaune.

Lamarin, Wanda ya faru misalin karfe 1:50 na Rana, ya hada da jefe jefen kujeru da kuma fadace-fadace.

Ba a gano mussababin faruwa rikcin ba. Wadanda ke a haraban sun tsere, yayinda yan sanda suka kore yan iskan daga wajen.

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin PDP a Lagas inda yan daba ke ta jifan junansu da kujeru

Yanzu Yanzu: Rikici ya barke a gangamin PDP a Lagas inda yan daba ke ta jifan junansu da kujeru
Source: UGC

Lamarin ya fara ne a lokacinda aka soma mikawa yan takaran mukaman majalisa tutar jam’iyya.

A cewar mai gabatarwa: “naga alamun wassu sun zo nan ne don tayar da hankali. Za a hukunta Wadanda suka zo nan don tada hankali a matsayin masu laifi.”

KU KARANTA KUMA: Buhari kadai muke goya ma baya a APC – SDP ta gargadi mambobinta

An chaje kowa kafin shiga cikin filin wasan gabannin fara shirin. Haka zalika, an hango wasu matasa na shan ganye a haraban, yayinda aka baiwa masu siyar da Kayan ruwa izinin siyar da kayan maye.

Ana kyautata zaton cewa dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar zai gabatar da jawabai nan da yan guntun lokaci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel