Mummunan rikicin siyasa ya kaure tsakanin ‘Yan APC da PDP a Ekiti

Mummunan rikicin siyasa ya kaure tsakanin ‘Yan APC da PDP a Ekiti

Mun samu labari maras dadi dazu nan cewa an yi fada tsakanin wasu Magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da kuma wadanda ke tare da jam’iyyar adawa ta PDP a wani gari a cikin jihar Ekiti kwanan nan.

Mummunan rikicin siyasa ya kaure tsakanin ‘Yan APC da PDP a Ekiti

Wasu 'Yan PDP sun kai wa Magoya bayan APC hari a Ekiti
Source: Twitter

The Nation ta rahoto cewa rikicin ya kaure ne a cikin garin Omuo Ekiti a karamar hukumar Ekiti ta gabas. Yanzu haka an kirga fiye da mutum 20 wadanda su ka samu rauni a dalilin wannan mugun rikici da ya kaure jiya Litinin.

Wannan abu ya faru ne sa’ilin da magoya bayan ‘dan takarar kujerar Sanata na yankin Kudancin Ekiti, Dayo Adeyeye da kuma Magoya bayan Femi Bamisile wanda shi ne ‘dan takarar majalisar tarayyan birnin su ke taron kamfe.

KU KARANTA: Manyan Jiga-jigan APC sun yi shirin raba Kwara da Saraki

Rikicin ya kaure ne lokacin da wasu ‘yan daba su ka shigo cikin masu yawon yakin neman zaben inda su ka shiga sarar su. Ana zargin cewa wadanda su kayi wannan aika-aika, yaran Sanara Biodun Olujunmi ta jihar ne.

Daga cikin wadanda aka yi wa rauni akwai manyan magoya bayan APC irin si Adeniyi Saliu , Kayode Ojo da kuma wani Adeniyi Ayo, wadanda aka ji wa ciwo a kai da ciki har da kuma baya. Yanzu haka dai su na kwance a asibiti.

Wadanda aka kai wa farmaki su na jinya ne a asibitin koyan aiki na jami’ar Ekiti da ke cikin Garin Ado Ekiti inda ake kokarin ceto rayukan su. Yanzu dai ‘yan sanda sun bazama neman wadanda su kayi wannan mummunan aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel