2019: Jerin wadanda ba za su yi zabe ba a bana

2019: Jerin wadanda ba za su yi zabe ba a bana

A yayin da ya rage kwanaki biyar kacal a gudanar da zaben kasa na ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, wani hasashe ya bayyana yadda wasu al'ummar Najeriya ba za su samu damar jefa kuri'un su a yayin babban zaben.

Kwanaki kadan da suka gabata ne aka fara yada wata 'yar almara a zaurukan sada zumunta, inda fitataccen Malamin nan da ya shahara a kan nazarin nahawu da adabi na harshen Turanci, Farfesa Sole Soyinka ya yi sharhi dangane da wadanda ba za su samu damar jefa kuri'un su ba a babban zabe na kasa.

2019: Jerin wadanda ba za su yi zabe ba a bana

2019: Jerin wadanda ba za su yi zabe ba a bana
Source: UGC

Binciken babban Farfesan na Turanci ya tabbatar da cewa, akwai adadin al'ummar Najeriya da kuri'ar su ta zamto haramiya ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, da kuma dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Shafin jaridar The Punch ya ruwaito cewa, madogara ta wannan bincike ta takaita ne kadai dangane da yadda wasu ke kan akida da kuma ra'ayi na dandana salon jagorancin wasu jam'iyyun na daban da jam'iyyar PDP da kuma ta APC.

Kazakila a yayin da al'ummar Najeriya ke ci gaba da shiryen-shiryen fitowa kwansu da kwarkwata wajen jefa kuri'u yayin zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da za a gudanar a ranar Asabar ta wannan mako, wani bincike ya tabbatar da cewa akwai wadanda ba za su samu ikon jefa kuri'un su ba sakamakon wasu dalilai da ba hakan suka so ba.

KARANTA KUMA: Rayuka 9 sun salwanta, Mutane 15 sun jikkata yayin aukuwar wani hatsari a jihar Kano

Binciken manema labarai na jaridar The Punch ya wassafa jerin wadanda suka afka cikin wannan rukuni na rashin samun dama ta jefa kuri'un su da suka hadar da; ma'aikatan lafiya, wasu daha cikin jami'an musamman dakarun soji da ke filin daga wajen yakar ta'addanci.

Sauran wadanda rashin samun dama ta jefa kuri'u a zaben bana ta shafa sun hadar da; gajiyayyu cikin al'umma, masu cutar kuturta, da kuma marasa lafiya da ke jinya a gidajen su ko kuma asibitoci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel