Kurmus: Wuta ta kone kayan aikin zabe da aka kai jihar Anambra, hotuna

Kurmus: Wuta ta kone kayan aikin zabe da aka kai jihar Anambra, hotuna

A yau, Talata, ne da misalign karfe 2:30 na rana gobara ta tashi a hedikwatar hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Gobarar ta yi sanadiyar konewar wasu kwantaina guda biyu da ke dauke da kayan aikin zabe da aka kai jihar.

Na’urorin tantance ma su zabe ne su ka fi yawa a cikin kwantainonin da wutar ta kone.

Tashin gobarar ya tilasta ma’aikatan INEC tsere wa daga ofisoshin su.

Kurmus: Wuta ta kone kayan aikin zabe da aka kai jihar Anambra, hotuna

Wuta a ofishin INEC na jihar Anambra
Source: Twitter

Kurmus: Wuta ta kone kayan aikin zabe da aka kai jihar Anambra, hotuna

Kurmus: Wuta ta kone kayan aikin zabe da aka kai jihar Anambra, hotuna
Source: Twitter

Kurmus: Wuta ta kone kayan aikin zabe da aka kai jihar Anambra, hotuna

Kurmus: Wuta ta kone kayan aikin zabe da aka kai jihar Anambra, hotuna
Source: Twitter

Ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, ma’aikatan hukumar kasha gobara na can sun a kokarin kasha gobarar.

Jami’an tsaro da su ka hada da ‘yan sanda da sojoji sun garzaya domin bayar da agaji a sakatariyar ta INEC.

DUBA WANNAN: Zalunci: An kama wasu ma’aikatan INEC da laifin karbar kudin ma su katin zabe

Sai dai ma’aikatan na INEC sun ki yarda su yi Magana da manema labarai yayin da aka nemi jin ta bakin su dangane da tashin gobarar.

Peter Obi, abokin takarar Atiku a jam'iyyar PDP, ya fito ne daga jihar Anambra kuma ya taba zama gwamna har sau biyu a jihar.

Ana cigaba da samun yawaitar tashin gobara a ofisoshin INEC da ke sassan kasar nana a yayin da zabe ya rage kwana uku kacal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel