Asarar kujeru 50 a APC: Buhari ya bayyana rashin jin dadin sa

Asarar kujeru 50 a APC: Buhari ya bayyana rashin jin dadin sa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa a game da hukuncin da kotun koli ta zartar na hana jam'iyyar All Progressives Congress, APC, shiga wasu zabukan da za a gudanar a zaben 2019.

Buhari ya bayyana ra'ayinsa a kan batun ne a yayin kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Rivers a yau Talata.

Shugaban kasar ya ce, "Na damu matuka a kan hukuncin da aka zartar na hana jam'iyyar mu gabatar da 'yan takara a wasu zabuka. Bani haufi cewa al'umma ne suka zabe ni amma ya zama dole in girmama hukumomin da na gada. Ina rokon ku kasance masu hakuri da juriya. Za mu tabbatar an yiwa kowa adalci a kasar nan."

DUBA WANNAN: Dattawan Arewa ba su goyi bayan Atiku ba - Junaidu

Asarar kujeru 50 a APC: Buhari ya bayyana rashin jin dadin sa

Asarar kujeru 50 a APC: Buhari ya bayyana rashin jin dadin sa
Source: Twitter

Hukuncin ne kotun koli ya nuna cewa jam'iyyar ta APC ta rasa kujeru 32 a majalisar dattawa, kujeru 13 a majalisar wakilai, kujeru uku na sanatoci da kujera daya na gwamna da mataimakinsa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki al'umma su cigaba da hakuri dashi a yayin da ya ke kokarin kawo gyra a kasar.

Ya kuma kara da cewa zai tabbatar an tura dakarun sojoji da jami'an 'yan sanda zuwa dukkan jihohin kasar domin ganin 'yan Najeriya sun kada kuri'unsu cikin ba tare da barazana ko tsoro ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel