2019: Wasu Kiristoci a Arewa sun yi wa Atiku Abubakar mubaya’a

2019: Wasu Kiristoci a Arewa sun yi wa Atiku Abubakar mubaya’a

Wata kungiya ta Kiristoci da Malaman addini a Arewacin Najeriya sun nuna goyon bayan su ga ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar a zaben 2019 da za ayi. Kungiyar ta cin ma wannan matsaya ne kwanan nan.

2019: Wasu Kiristoci a Arewa sun yi wa Atiku Abubakar mubaya’a

Malamai da Kiristocin da ke Arewa sun ce ba za su zabi Buhari ba
Source: UGC

Kungiyar ta ACIPA ta zauna a Garin Jos a Ranar Lahadin nan inda ta tsaida cewa mabiyan ta za su zabi Atiku Abubakar ne a zaben shugaban kasa da za ayi bana. Kungiyar tace ta tabbata ba Buhari ke rike da karagar kasar ba.

Haka kuma kungiyar ta nuna rashin gamsuwa da gwamnatin APC inda ‘Yan Arewa kuma Musulmai ne musamman ke rike da mukaman da su ka shafi sha’anin tsaro. Kungiyar tace an kuma taso wasu ‘ya ‘yan ta gaba a kasar.

KU KARANTA: Ni na hana Tinubu zama Mataimakin Buhari saboda duk Musulmai ne-Saraki

Daga cikin wadanda ACIPA ta ke kukan an muzgunawa akwai Sanata Dino Melaye da kuma Alkalin Alkalan Najeriya. Rabararen Luke Shehu wanda shi ne shugaban kungiyar ya fitar da wannan jawabi a karshen makon jiya.

Kiristocin yankin sun kuma koka da kalaman da wani gwamna yake yi da ke nuna cewa za a hallaka wadanda su ka jefa kan su cikin harkar zaben Najeriya don haka su ka nemi manyan Duniya su sa ido game da zaben na Najeriya.

Sai dai kuma kungiyar Northern Discuson Group (NDG) tayi wani zama irin wannan a dakin taro na Arewa House a Kaduna inda bayan ta kai ta kawo tace ya kamata jama’a su sake marawa Buhari baya ne a zaben domin ya gyara kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel