Cikin Hotuna: Taron yakin zaben Atiku a jihar Legas

Cikin Hotuna: Taron yakin zaben Atiku a jihar Legas

A yayin da ya rage saura kwanaki biyar kacal a gudanar da babban zaben kasa na ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da taron sa na yakin zabe cikin jihar Legas.

Kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa, dubunnan masoya da magoya baya sun yi turutuwa wajen yiwa Atiku kyakkyawar tarba yayin taron sa na yakin zabe a gidauniyar taro Tafawa Balewa da ke babban birni na jihar Legas.

Atiku da Uwargidan sa, Titi, yayin yakin zabe a jihar Legas

Atiku da Uwargidan sa, Titi, yayin yakin zabe a jihar Legas
Source: Twitter

Taron yakin zaben Atiku a jihar Legas

Taron yakin zaben Atiku a jihar Legas
Source: Twitter

Tururuwar al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Legas

Tururuwar al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Legas
Source: Twitter

Atiku da jiga-jigan PDP yayin taron yakin zabe a jihar Legas

Atiku da jiga-jigan PDP yayin taron yakin zabe a jihar Legas
Source: UGC

Cikin jawaban sa Atiku ya yi tsokaci dangane da gazawar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na samar da ingataccen tsaro a fadin kasar nan da kuma zagwanyewar tattalin arzikin ta.

KARANTA KUMA: Rayuka 9 sun salwanta, Mutane 15 sun jikkata yayin aukuwar wani hatsari a jihar Kano

Tawagar Atiku yayin yakin zaben sa a jihar Legas ta hadar da abokin takarar sa, Peter Obi, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, da kuma shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel