Miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Mata guda 2 a Kaduna

Miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Mata guda 2 a Kaduna

Wasu gungun yan bindiga da ba’a san daga inda suka fito ba sun yi awon gaba da wasu yan mata biyu yan gida daya a unguwar Kudenda ta jahar Kaduna dake cikin karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matan da ba’a bayyana sunayensu ba sun hada da yar shekara 18 da kanuwrta mai shekaru 13, an sacesu ne da yammacin ranar Litinin, 11 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Kada ku jefa jahar Kano cikin fitina – Sarki Sunusu II ga yan siyasan Kano

Sai dai majiyar ta bayyana cewa har yanzu yan bindigan basu tuntubi iyalan yan matan game da batun biyan kudin fansa don karbarsu ba, sai dai iyalan yan matan sun tabbatar mata da cewa tuni Yansanda sun kaddamar da bincike akan lamarin tare da kokarin ceto yan matan.

Ko a ranar Litinin, 11 ga watan Feburairu sai da wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai suka halaka wani Malami dake koyarwa a wata jami’a mai zaman kanta, BOWEN dake garin Iwo cikin jahar Osun

Sai dai yan bindigan basu tsaya nan ba, sai da suka yi awon gaba da wasu Malaman jami’ar ta BOWEN su biyu da nufin yin garkuwa dasu har sai an biyasu makudan kudade a matsayin kudaden fansa kafin su sakesu, kamar yadda suka saba.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Osun, DSP Folashade Odoro ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace tuni kwamishinan Yansandan jahar ya tura wasu jami’an Yansanda hanyar Iwo zuwa Osogbo, inda lamarin ya faru da nufin gano inda Malaman suke.

A wani labarin kuma wasu gungun masu garkuwa da mutane ne suka gamu da bazata daga hannun jama’a kauyen Gidan Garkuwa dake cikin karamar hukumar Sabuwa ta jahar Katsina, inda jama’an garin suka nuna jarumta, suka fuskancesu, har suka kashe mutane biyar daga cikinsu.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Feburairu da misalin karfe 1 na dare, a lokacin da yan bindigan sika isa kauyen, inda suka fara harbe harbe a iska da nufin tsoratar da jama’an, tare da yi musu dauki daidai kamar yadda suka saba, har sai an biyasu kudin fansa, amma sai reshe ya juye da mujiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel