Buhari kadai muke goya ma baya a APC – SDP ta gargadi mambobinta

Buhari kadai muke goya ma baya a APC – SDP ta gargadi mambobinta

- Tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu goyon bayan jam’iyyar Social Democratic Party (SDP)

- Shugaban jam’iyyar SDP a karamar hukumar Ughelli a jihar Delta, Jonathan Idoro ya bayyana cewa jam’iyyar tana goyawa shugaba Buhari baya saboda ta gaza tsayar da dan takaran kujeran shugaban kasa a kan lokaci

- A cewar Idoro, za a hukunta duk wani dan jam’iyyar SDP da aka kama da shirin tsayar da wani dan takara

Jam’iyyar Social Democratic Party a Ughelli kudancin karamar hukumar jihar Delta, a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu ya bayyana rashin goyawa wani dan takara baya a jam’iyyar All Progressive Congress (APC) da ya wuci shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar ta bayyana a wani jawabi da shugabanta Jonathan Idoro ya gabatar, jam’iyyar bata marawa dan takaran kujerar wakilai a jam’iyyar APC, Francis Waive baya ba.

Kamfanin Dillancin labarai (NAN) ya rahoto cewa Idoro yace ya kasance mai goyon bayan Hon. Solomon Awhinawhi dan takaran jam’iyyar SDP a majalisan wakilai.

Buhari kadai muke goyon baya a APC – SDP ta gargadi mambobinta

Buhari kadai muke goyon baya a APC – SDP ta gargadi mambobinta
Source: Twitter

A cewar shi, uwar jam’iyyar na kasa ta amince da goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari kadai a zaben shugaban kasa.

Haka zalika, yayi gargadi cewa akwai hukuncin da aka tanadar wa duk dan jam’iyyar da aka kama da shirin marawa dan wata jam’iyya baya a sauran zabukan kasar bayan na Buhari.

KU KARANTA KUMA: Kada ku sa mu cikin masu goyon bayan Buhari – Kungiyar Musulunci

A wani lamari na daban, mun ji cewa wata kungiya mai suna Egalitarian Mission for Africa ta shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ta kalubalanci lamarin barin dan takarar PDP, Atiku Abubakar ya yi takara zaben shugaban kasa.

Olukayode Ajulo, tsohon sakataren jam’iyyar Labour Party wanda ya kaddamar da oyon bayansa ga abokin adawar Atiku, Shugaban kasa Muammadu Buari a zabe mai zuwa ne shugaban kungiyar.

A takardar karan, kungiyar tace Atiku wanda ke yiwa jam’iyyar PDP takara a zabe mai zuwa ba asalin dan Najeriya bane don aka bai cancanci takara ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel