Jifan Buhari da aka yi a jiya: APC na fushi da gwamna Amosun

Jifan Buhari da aka yi a jiya: APC na fushi da gwamna Amosun

- Jam'iyyar APC tayi alkawarin daukar mataki akan rashin da'ar da aka gwada mata a jihar Ogun

- Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa yace jam'iyyar APC tana da dokoki kuma ba wanda zai karya su ya zauna lafiya

- Ana zargin gwamna Ibikunle Amosun da hayar mutane don tozarta shugaba Buhari da wasu jiga jigan jam'iyyar

Jifan Buhari da aka yi a jiya: APC na fushi da gwamna Amosun

Jifan Buhari da aka yi a jiya: APC na fushi da gwamna Amosun
Source: Depositphotos

A jiya ne ddai a jihar aka ga wasu bata gari suna jifan shugaba Buhari da leda da shirgi, lamari da ya sanya masu tsaronsa har hudu suka kare shi.

Jam'iyyar APC tayi alkawarin daukar tsautsauran mataki akan wadanda suka dau nauyin hayaniya da hargitsin da ya faru a kamfen din jihar Ogun.

Sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar, Malam Lanre Issa-Onilu yace jam'iyyar tayi dana sanin harin da aka kaiwa shugaba Buhari da wasu jiga jigan jam'iyyar wanda ake zargin gwamna Ibikunle Amosun ne ya dau nauyi.

Issa-Onilu, yace hakan babban laifi ne kuma babu wanda yafi karfin dokokin jam'iyya don tilas ne bin su.

GA WANNAN: Kyan yaba alheri, riqe amana: Masu fanshon Nigeria Airways sun shirya wa zaben makon gobe tsaf!

Mai magana da yawun jam'iyyar wanda ya shawarci mutane da kada su damu ko daga hankalin su akan abin ashshan da ya faru a ranar litinin din yace zasu cigaba da zagayen kamfen din kuma a fito kwai da kwarkwata don zaben yan jam'iyyar APC a zaben mai zuwa.

"Wannan wani nau'i ne na rashin da'a. APC kuma bazata lamunci hakan ba daga duk wani Dan jam'iyyar komai kuwa matsayin shi. Jam'iyyar zata kara duba yanda aka ajiye zaune gari banza tare da shirya musu yanda zasu tozarta tare da kai hari ga shugaban kasa da kuma shuwagabannin jam'iyya. Jam'iyyar zata dau mataki ana kammala zabe."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel