Clinton ya fasa zuwa Najeriya ne saboda kalaman Nasiru Elrufai na tunzura jama'a - PDP

Clinton ya fasa zuwa Najeriya ne saboda kalaman Nasiru Elrufai na tunzura jama'a - PDP

- Bill Clinton ya fasa kawo ziyarar da yayi niyya

- Jam'iyar PDP tana zargin APC akan wannan abu

- Clinton zai halarci wajen sanya hannun yarjejeniyar zaman lafiya da Atiku da Buhari zasuyi

Zabe: Bai kamata a bari APC

Zabe: Bai kamata a bari APC
Source: UGC

Mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP Paul Ibe yana zargin jam'iyar APC akan fasa kawo ziyara da tsohon shugaban kasar US Bill Clinton yayi.

Ana tunanin Clinton zai halarci wajen sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin shugaban kasa Muhammad Buhari da Atiku Abubakar.

Kwamitin samar da zaman lafiya ta kasa (NPC) ta shirya wannan shiri ne tare da zabe da zai gudana.

Sai da lokacin ya gabato Clinton yace bayaso ziyarar tashi ta zamto tamkar ta siyasa.

GA WANNAN: Boko Haram: Yankin mazaba ta yanzu babu matsalar tsaro - Sanata Binta ta Adamawa

Da yake maida martani Ibe yace fasawar tashi tana da alaka da wasu maganganu da suka fito daga jam'iyar hamayya.

"Mun shiga cikin bacin rai bayan mun samu sakon cewa tsohon shugaban kasar US Bill Clinton bazai samu damar kawo ziyara Najeriya ba bisa wasu maganganu da suka fita".

"Mun fahimci dalilin Clinton musamman furucin ' Jakar gawa' sannan muna fatan komai zai warware danya samu zuwa".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel