Duk abinda PDP ke shirya wa a Legas a shirye muke da martani - Amaechin APC

Duk abinda PDP ke shirya wa a Legas a shirye muke da martani - Amaechin APC

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya zargi gwamnan Rivers da cin amana

- Amaechi yace ba zai koma Abuja ba sai anyi zaben ranar asabar

- Asabar ranar mu ce, inji Amaechi

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Source: UGC

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya zargi gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da jan ra'ayin shari'a akan juyawa APC baya a jihar.

Amaechi wanda yayi maganar a zagayen kamfen din shugaban kasa a fatakwal a ranar talata, ya zargi cewa gwamnan yaci amanar shi bayan shi ya mika shi har aka bashi minista a mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kamar yanda ministan ya fada, sojoji sunyi yunkurin kama shi a 2015 duk da yana da kariya a matsayin gwamna a lokacin. Ya kara da cewa yaki tsakanin shi da Wike yanzu aka fara.

Yace, "Duk abinda Wike ke so a ranar asabar, zamu bashi. Ko mene ne PDP ke so a jihar Rivers, a shirye muke zamu basu. Abu ne mai sauki. Abin ya kai ga in da sai mutum ya tsayu da kyau. Ranka shi dade, bazan koma Abuja ba, ina nan har sai ranar zabe,"

GA WANNAN: Kabilar Fulani sunyi wa Buhari alkawarin kuri'u 11m a makon gobe

"Abinda muke so shine kawai shugaban kasa ya gode mana idan mun gama. A shirye muke. Sun kashe mana mutane, yan APC, kullum kashe su akeyi."

Kamar yanda Amaechi yace, kashi 80 na wadanda sukayi nasara a siyasar jihar Rivers sun bi ta hannun shi.

"Wike shine shugaban ma'aikata na. Ni na sashi ya zama shugaban kansiloli. Na zabe shi a matsayin minista. Da yaga Goodluck sai yaci amanata. Anci amanata da yawa, har wasu sanatoci ma. Bayan ka gama taimakon su, kayi musu addu'a, sai suje suci amanarka saboda kankanin abu. Asabar ranar mu ce," inji shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel