Yaki da kake da rashawa yana bisa tsari, dattijon Bayelsa ya fadi ma Buhari

Yaki da kake da rashawa yana bisa tsari, dattijon Bayelsa ya fadi ma Buhari

- Yakin da Buhari yayi akan hanci da rashawa da rashawa ya fidda Najeriya daga kunyar idon duniya

- King Alfred yace suna alfahari da Buhari

- Shugaban kasar yakai ziyarar yada manufa jihar Bayelsa

Yaki da kake da rashawa yana bisa tsari, dattijon Bayelsa ya fadi ma Buhari

Yaki da kake da rashawa yana bisa tsari, dattijon Bayelsa ya fadi ma Buhari
Source: Depositphotos

Sarakunan gargajiya na jihar Bayelsa sunyi jinjina ga shugaban kasa Muhammad Buhari bisa yaki da cin hanci da rashawa da yayi a kasar nan.

Sarakunan sun bayyana hakan ne a sakateriyar su dake Yenagoa a lokacin da suke karbar bakuncin Buhari.

Shugaban kasar ya kai ziyara jihar ne dan yada manufar sa na kara tsayawa takara.

Idan bamu manta ba shugaban kasa Muhammad Buhari ya kada abokin karawar sa Goodluck Ebele Jonathan a shekara ta 2015 a lokacin da yayi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa.

GA WANNAN: EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abokan damfararta a Abuja

Da yake magana a madadin sarakunan ciyaman na sarakunan gargajiyar jihar ta Bayelsa King Alfred Diete Spiff yace suna alfahari da shugaban kasar.

"Yaki da cin hanci da rashawa da kayi ya fitar da Najeriya daga kunyar idon duniya" sarkin ya fadawa Buhari.

Sarkin ya kasance gwamnan soja na farko a jihar Rivers ya bayyanawa shugaban kasar goyan bayan sarakunan gargajiyar bisa ga wannan tafiya tasa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel