Kungiyar ASUP ta janye yajin aiki bayan wata biyu

Kungiyar ASUP ta janye yajin aiki bayan wata biyu

Kungiyar malaman kwalejin kimiyya (ASUP) sun janye yajin aikin da su ka shafe watanni sun a yi bisa gazawar gwamnatin tarayya na cika yarjejeniyr da su ka kulla tun a cikin shekarar 2017.

Da ya ke jawabi ga manema labarai bayan kamala taron shugabannin kungiyar (NEC) da aka yi yau, Talata, a Abuja, sakataren ASUP, Usman Dutse, ya bukaci dukkan ‘ya’yan kungiyar da su koma bakin aikin su daga gobe, Laraba.

A cikin makon jiya ne kungiyar malaman makarantun jami'o'i (ASUU) ta janye yajin aikin da ta shafe watanni uku ta na yi.

Sai dai, sakataren na ASUP bai bayyana dalilan kungiyar na yanke shawarar janye yajin aikin ba.

Kungiyar ASUP ta janye yajin aiki bayan wata biyu

Shugabannin kungiyar ASUP
Source: Twitter

A nata bangaren, kungiyar ASUU ta ce ta janye yajin aikin ne bayan wata gana wa da wakilan gwamnatin tarayya da ministan kwadago da samar da aiyuka, Sanata Chris Ngige, ya jagoranta.

ASUU ta ce ta janye yajin aikin ne bayan kamala tuntuba da tattauna wa a kan tayin da gwamnatin ta yi a kan bukatun da kungiyar ta bukaci a cika ma ta kafin ta koma bakin aiki.

DUBA WANNAN: Zabe: INEC ta warware kokonton ‘yan Najeriya a kan na’urar tantancewa

A sanarwar da ta fitar, ASUU ta ce bayan amince wa da gwmnatin tarayya ta yi na sakin biliyan N20 domin biyan malaman jami’o’i bashin alawus da su ke bi a shekarar 2018, gwamnatin ta yi alkawarin sake fitar da wata biliyan N25bn a watan Afrilu zuwa Mayu na shekarar nan, bayan haka kuma gwamnatin za ta cigaba da zartar da yarjejeniyar da su ka kulla da ASUU tun shekarar 2013.

ASUU ta yi godiya ga kungiyoyi daban-daban, musamman kungiyar kwadago, bisa goyon baya da hadin kan da su ka ba su yayin yajin aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel