2019: Jama’an Arewa sun amsa kiran Atiku Abubakar – Shugaban PDP

2019: Jama’an Arewa sun amsa kiran Atiku Abubakar – Shugaban PDP

- Uche Secondus yace har a cikin Garin Daura ana son Atiku Abubakar

- Shugaban Jam’iyyar yake cewa dinbin Mutanen Arewa za su zabi PDP

2019: Jama’an Arewa sun amsa kiran Atiku Abubakar – Shugaban PDP

Shugaban PDP Prince Secondus yace Atiku yana da mutane a Katsina
Source: Twitter

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP na kasa baki daya, Prince Uche Secondus, ya bayyana cewa sun gamu da wasu manyan masoyan ‘dan takarar PDP Atiku Abubakar a cikin Daura a lokacin da su ka tafi yawon kamfe a jihar Katsina.

Uche Secondus, yake cewa har a Mahaifar shugaban kasa Buhari, ‘dan takarar na su yana da dinbin Magoya baya a Garin na Katsina. Secondus ya bayyana wannan ne a wajen kamfen din PDP da aka yi jiya Litinin a jihar Ribas.

KU KARANTA: Kowa ya zabi duk ‘Dan takarar da ku ka ga dama - Buhari

Shugaban na PDP na Najeriya ya fadawa mutanen Ribas cewa Atiku Abubakar yana da Masoya ba a Arewacin Najeriya kurum ba, har da ma z Kauyen Daura inda nan aka haifi shugaban kasa Buhari wanda yake neman tazarce.

Prince Secondus ya kara da cewa irin jama’an da aka gani wajen taron PDP a Kano ya soma bayyana nasarar da jam’iyyar za ta samu a zaben da za ayi. Shugaban jam’iyyar adawar yace mutanen Arewa sun yi na’am da tafiyar Atiku.

Secondus yake cewa ya ragewa jama’a su zabi wanda zai yi shugabanci yadda ya kamata da kuma wanda wasu mutane dabam su ka zagaye sa, su ke abin da su ka so a gwamnatin sa, inda ya kuma gargadi APC game da magudin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel