Da duminsa: Jiragen NAF sun fara yiwa INEC jigilar kayayakin zabe, hotuna

Da duminsa: Jiragen NAF sun fara yiwa INEC jigilar kayayakin zabe, hotuna

- Rundunar Sojin Saman Najeriya, NAF, na taka muhimmiyar rawa domin ganin an gudanar da zaben 2019 cikin sauki

- Tuni dai NAF ta fara taimakawa Hukumar INEC wurin jigilar kayayakin zabe zuwa jihohi daban-daban

- NAF ta bayar da jiragen ne domin jigilar kayayakin zaben INEC zuwa wasu wurare da ke da wahalar zuwa

A yau Litinin 11 ga watan Fabrairu ne Rundunar Sojin Saman Najeriya NAF ta fara taimakawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC jigilar kayayakin zaben ta zuwa wasu jihohin Najeriya domin gudanar da zaben 2019.

Legit.ng ta gano cewa za a gudanar da jigilar kayayakin zaben da rana da kuma cikin dare inda za ayi amfani da jirgin NAF C-130 Hercules da ke tashi daga filin tashi da saukan jirage na Nnamdi Azikwe da ke Legas zuwa jihohin Najeriya.

A cewar sanarwar da ta fito daga Kakakin NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce za ayi amfani da C-130 H wurin jigilar kayayakin zaben da za a mika su ga jami'an INEC da CBN da jami'an tsaro da ke jira a filayen jiragen sama na jihohi.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa al'ummar Adamawa za su zabi Buhari - Talban Adamawa

Da duminsa: Jiragen NAF sun fara jigilar kayayakin zabe

Da duminsa: Jiragen NAF sun fara jigilar kayayakin zabe
Source: Facebook

Idan ba a manta ba a kwanakin baya, Shugaban hafsin sojojin sama na Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar ya ce NAF a shirye take domin taimakawa INEC wurin jigillar kayayakin zabe zuwa wurare daban-daban kamar yadda ta saba yi a zabukkan da suka gabata.

An bayar da jiragen ne kawai domin jigilar kayayakin zabe a yunkurin NAF na bayar da gudunmawarta wurin gudanar da zabe.

Da duminsa: Jiragen NAF sun fara jigilar kayayakin zabe

Da duminsa: Jiragen NAF sun fara jigilar kayayakin zabe
Source: Facebook

Da duminsa: Jiragen NAF sun fara yiwa INEC jigilar kayayakin zabe, hotuna

Da duminsa: Jiragen NAF sun fara yiwa INEC jigilar kayayakin zabe, hotuna
Source: Facebook

A bangarensa, Sufeta Janar na 'yan sanda, IGP Mohammed Adamu ya bayar da umurnin a baza jami'an yan sanda da za su rika aikin samar da tsaro a dukkan ofisoshin INEC da ke jihohin Najeriya.

Hakan na cikin wata sanarwa ce da Kakakin 'yan sandan Najeriya, ACP Frank Mba ya aikewa Legit.ng a ranar Lahadi 10 ga watan Fabrairun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel