Zaben 2019: INEC ta fitar da jerin laifukan zabe 15

Zaben 2019: INEC ta fitar da jerin laifukan zabe 15

Kwanaki kadan kafin ranar babban zaben shekarar 2019, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta fitar da jerin laifuka da ake gargadin masu kada kuri'a su guji aikatawa yayin zabe.

Hukumar zaben ta yi wannan sanarwar ne a cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa ta shafinta na Twitter mai suna @inecnigeria.

Zaben 2019: INEC ta fitar da jerin laifukan zabe 15

Zaben 2019: INEC ta fitar da jerin laifukan zabe 15
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da ba su taba sauya sheka ba

Ga jerin laifukan zaben a kasa

1. Kada kuri'a sau biyu

2. Yiwa kananan yara da shekarunsu bai kai 18 ba rajista

3. Tayar da hankalin al'umma

4. Amfani da katin zaben da ba naka ba

5. Sanar da sakamakon zabe na karya

6. Yin kamfen a ranar zabe

7. Saye da sayar da kuri'a/kuri'u

8. Kawo cikas yayin gudanar da zabe

9. Hana masu zabe kayar da kuri'arsu

10. Sace akwatin zabe ko wasu kayayakin zaben

11. Lalata kayayakin zabe

12. Yin zabe sau biyu

13. Kada kuri'u na bogi

14. Barazana, cin zarafi ko dukkan ma'aikatan zabe

15. Hana al'umma kada kuri'arsu

Hukumar zaben ta ce: "Kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yiwa kwaskwarima ya zama Electoral Act 2010 da kuma dokokin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa INEC sune dokokin da ke tafiyar da yadda ake gudanar da zabe a Najeriya."

A baya, Legit.ng ta kawo muku samfurin takardan kada kuri'a ta hukumar INEC ta fitar gabanin zaben da za a gudanar a ranar 16 ga watan Asabar na shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.

Hukumar ta fitar da wannan sanarwar ne ta shafinta na Twitter a ranar Litinin 11 ga watan Fabrairun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel