Hotuna: An fara shiri, hukumar Sojin ta fara raka kayayyakin zabe jihohin Najeriya

Hotuna: An fara shiri, hukumar Sojin ta fara raka kayayyakin zabe jihohin Najeriya

Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC tare da hadin kan hukumar sojojin saman Najeriya wato NAF sun fara tashi da kayayyakin da za'ayi amfani da su wajen zaben shugaban kasa da yan majalisan tarayya ranan Asabar, 16 ga watan Febrairu, 2019.

Hukumar sojin saman ta kaddamar da amfani da jirgin samanta wajen raka kayayyakin ne fari daga ranan Litinin, 11 ga watan Febrairu, 2019.

Legit Hausa ta samu wannan labari ne daga mai magana da yawun hukumar Soji, Ibikunle Daramola inda yace:

"Hukumar sojin Najeriya a jiya, 11 ga watan Febrairu, 2019 ta fara dauka kayayyakin zaben hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC zuwa jihohin Najeriya daban-daban domin gudanar da zaben 2019."

Za'a kai wadannan kayayyaki cikin dare da ranan da jirgin NAF C-130 Hercules daga babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja zuwa dukkan filayen jiragen da Najeriya."

Za ku tuna cewa babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya bayyana a wata ganawa cewa hukumar sojin shirye take da hada kai da hukumar INEC wajen tafiyar mata da kayayyakin zabe kamar yadda aka saba."

Kalli hotunan:

Hotuna: An fara shiri, hukumar Sojin ta fara raka kayayyakin zabe jihohin Najeriya

Kayayyakin zabe
Source: Facebook

Hotuna: An fara shiri, hukumar Sojin ta fara raka kayayyakin zabe jihohin Najeriya

Jirgin daukan kayayyakin
Source: Facebook

Hotuna: An fara shiri, hukumar Sojin ta fara raka kayayyakin zabe jihohin Najeriya

Hotuna: An fara shiri, hukumar Sojin ta fara raka kayayyakin zabe jihohin Najeriya
Source: Facebook

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel