Yabon Buhari: Tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya yiwa Jonathan gori

Yabon Buhari: Tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya yiwa Jonathan gori

- Tsohon gwaman jihar Bayelsa, Timipre Sylva ya ce albarkacin Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanya aka gina titi zuwa kauyen su tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Mr Sylva ya yi wannan furucin ne yayin kaddamar da yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari a garin Yenagoa

- Tsohon gwamnan ya tunatar da al'ummar jihar cewa tun a zaman su Sir Milford Okilo 'yan kabilar Ijaw ke hadin gwiwa da Arewa domin samar da ayyukan cigaba saboda haka ya bukaci su zabi shugaba Buhari da APC

Yabon Buhari: Tsohon gwamnan bayelsa ya yiwa Jonathan gori

Yabon Buhari: Tsohon gwamnan bayelsa ya yiwa Jonathan gori
Source: UGC

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva ya ce tabarakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne dalilin samar da titin kwalta zuwa kauyen su tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wato Otouke.

DUBA WANNAN: Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da ba su taba sauya sheka ba

A yayin da ya ke jawabi wurin kaddamar da yakin neman zaben takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Yenagoa, ya tunatar da mutane cewar tun zamanin Sir Milford Okilo, 'yan kabilar Ijaw suna hada kai da 'yan Arewa domin samar da ayyukan cigaba.

Ya shawarce su da su sake zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran 'yan takara a karkashin jam'iyyar APC a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Sylva ya ce: "Yanzu APC ta kara karfafa a jihar Bayelsa saboda gwazon Shugaban kasa Buhari. Albarcin shugaban kasa ce ta sanya aka gina titi zuwa Otuoke, kauyen tsohon Shugaban kasa Jonathan baya ga wasu ayyukan cigaba masu yawa da shugaban kasar ya samar a jihar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel