Dakarun Sojin Najeriya sun tarwatsa mayakan Boko Haram, sun kashe da dama

Dakarun Sojin Najeriya sun tarwatsa mayakan Boko Haram, sun kashe da dama

Dakarun rundunar Sojin Najeriya sun yi fata fata da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a ranar Asabar, 9 ga watan Feburairu yayin da yan ta’ddan suka lodo makamai cikin jerin gwanon motocin yaki da nufin kutsa cikin sansanin Sojojin.

Legit.ng ta ruwaito wannan lamati ya faru ne a da misalin karfe 6 na yammacin Asabar a sansanin Sojojin Najeriya dake karamar hukumar Madagali ta jahar Adamawa inda Sojojin cikin nuna kwanji da jarumta suka mayar ma yan ta’addan da biki, suka kashe na kashewa, suka raunata na raunatawa sauran kuma suka tsere.

KU KARANTA: Rikicin Obasanjo da Buhari: Gwamnan jahar Kaduna yayi karin haske

Dakarun Sojin Najeriya sun tarwatsa mayakan Boko Haram, sun kashe da dama

Dakarun Sojin Najeriya sun tarwatsa mayakan Boko Haram, sun kashe da dama
Source: Facebook

Sakamakon wannan mummunan asara da Sojojin suka tafka ma mayakan Boko Haram da kuma asarar makamansu ya baiwa Sojojin daman kare sansaninsu, inda suka kashe da dama, sa’annan suka kama wani guda daya, yayin da sauran suka tsere dauke da rauni daban daban.

Daga cikin makaman da Sojojin suka kwato akwai bindiga kirar AK 47 guda biyar, alburusai, bom gurnet, alburusai masu baro jirgi, wayoyin hannu da kuma wani na’urar daukan hoto guda daya da suke amfani dashi wajen yin bidiyon ta’addancinsu.

Daga bangaren Sojojin Najeriya kuwa, an samu wani Soja guda daya da kuma Sojan sa kai na civilian JTF guda daa da suka rasa ransu, haka zalika wasu Sojoji guda biyar sun samu rauni, kuma suna samun kulawa a asibiti yadda ya kamata.

Dakarun Sojin Najeriya sun tarwatsa mayakan Boko Haram, sun kashe da dama

Dakarun Sojin Najeriya sun tarwatsa mayakan Boko Haram, sun kashe da dama
Source: Facebook

Shima mukaddashin kwamandan runduna ta bakwai dake jibge a Maiduguri ya jinjina ma namijin kokarin da Sojojin Najeriya suka nuna, sa’annan ya jajanta ma iyalan Sojojin da suka mutu, inda ya tabbatar da cewa ba su sadaukar da ransu a banza ba.

A wani labarin kuma, babban shelkewatar rundunar Sojan kasa ta sanar da nadin Kanal Sagir Musa a matsayin sabon kaakakinta, wanda kafin nadin nasa shine kaakakin runduna ta 82 dake jibge a jahar Enugu.

Wannan nadi na Sagir Musa ya biyo bayan murabus na kashin kai da Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya yi ne a Alhamis din data gabata, 7 ga watan Feburairu, wanda hakan ya samar da bukatan maye gurbinsa da wanda ya cancanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel