Magoya bayan Buhari sun nemi kotu ta hana Atiku takara, cewa shi dan Kamaru ne

Magoya bayan Buhari sun nemi kotu ta hana Atiku takara, cewa shi dan Kamaru ne

- Wata kungiyar magoya bayan shugaba Buhari sun nemi kotu ta hana Atiku takara a zabe mai zuwa

- Kungiyar tayi zargin cewa Atiku wanda ke yiwa jam’iyyar PDP takara a zabe mai zuwa ba asalin dan Najeriya bane don aka bai cancanci takara ba

- Tace kundin tsarin mulki bata ba wanda ba dan kasa ba damar tsayawa takara ba

Wata kungiya mai suna Egalitarian Mission for Africa ta shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ta kalubalanci lamarin barin dan takarar PDP, Atiku Abubakar ya yi takara zaben shugaban kasa.

Olukayode Ajulo, tsohon sakataren jam’iyyar Labour Party wanda ya kaddamar da oyon bayansa ga abokin adawar Atiku, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa ne shugaban kungiyar.

A takardar karan, kungiyar tace Atiku wanda ke yiwa jam’iyyar PDP takara a zabe mai zuwa ba asalin dan Najeriya bane don aka bai cancanci takara ba.

Magoya bayan Buhari sun nemi kotu ta hana Atiku takara, cewa shi dan Kamaru ne

Magoya bayan Buhari sun nemi kotu ta hana Atiku takara, cewa shi dan Kamaru ne
Source: Facebook

Ajulo ne kuma jagoranci shiar da karar a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Kada ku sa mu cikin masu goyon bayan Buhari – Kungiyar Musulunci

Wadanda aka shigar karar da su sun ada da PDP, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da Abubakar Malami, ministan shari’a na Najeriya.

Kungiyar tayi korafincewa an haifi Atiku a ranar 25 ga watan Nuwamba a kauyen Jada wanda take a kasar Kamaru. Sannan cewa mahaifan Atiku duk yan Kamaru ne.

Sai dai ba a sanya ranar sauraron sari’anba duk da cewar saura kwanaki biyar a gudanar da zaben shugaban kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel