Yanzunnan: EFCC za ta ci gaba da tsare Babachir Lawal bisa umurnin kotu

Yanzunnan: EFCC za ta ci gaba da tsare Babachir Lawal bisa umurnin kotu

- Wata babbar kotun gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin cewa Mr Babachir Lawal, zai ci gaba da zama a hannun hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC

- Kotun ta sanya ranar Laraba, 13 ga watan Fabreru a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraro shari'ar

- Hukumar tana zargin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da aikata laifuka 10 da suka shafi hada baki tare da sama da fadi da kudaden gwamnati

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Abuja, ta bayar da umurnin cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mr Babachir Lawal, zai ci gaba da zama a hannun hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yiwa dukiyar gwamnati zagon kasa (EFCC).

Hakan na nufin cewa hukumar EFCC za ta ci gaba da tsare Mr Babachir Lawal, bayan da kotun a ranar Talata ta ki amincewa da bukatar bayar da belinsa.

Kotun ta sanya ranar Laraba, 13 ga watan Fabreru a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraro shari'ar.

KARANTA WANNAN: Zaben 16 ga watan Fabreru: Wata kungiyar Igbo ta goyi bayan Atiku

Yanzunnan: EFCC za ta ci gaba da tsare Babachir Lawal bisa umurnin kotu

Yanzunnan: EFCC za ta ci gaba da tsare Babachir Lawal bisa umurnin kotu
Source: UGC

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da kuma masu yiwa dukiyar gwamnati zagon kasa (EFCC) ta cafke tsohon gwamnatin tarayya (SGF) Babachir Lawal.

Hukumar tana zargin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da aikata laifuka 10 da suka shafi hada baki tare da sama da fadi da kudaden gwamnati, ta hanyar bayar da kwangilar bogi. Hukumar tana tuhumar Lawal ne tare da wasu mutane ukkuu da kamfanoni biyu.

Mutanen da kamfanonin da ake tuhumarsu tare da Lawal, sun hada da: Hamidu David Lawal; Sulaiman Abubakar; Apeh John Monday; kamfanin Rholavision Engineering Limited da kuma kamfanin Josmon Technologies Limited.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel