Kada ku sa mu cikin masu goyon bayan Buhari – Kungiyar Musulunci

Kada ku sa mu cikin masu goyon bayan Buhari – Kungiyar Musulunci

Kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky a jiya Litinin, 11 ga watan Fabrairu ta bayyana cewa bata taba goyon bayan takarar shugaban kasa Muhammadu Buari ba a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu kamar yadda wata kungiyar Shi’a mara tushe tayi hasashe.

A wata sanarwa daga Muhammad Ibrahim Gamawa na kungiyar a Najeriya yace: “Mun karanta sannan mun yi watsi da wani zargin cewa kungiyar matsan Shi’a a Katsina sunce kungiyar ta marawa takarar Buhari baya a zaben da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Sanarwar yace kungiyar Shi’a “bata taba mallakar kowace kungiya na siyasar matasa ba. Duk wata sanarwa da zamu yi yana fitowa ne daga majiuoyinmu wanda ba boyayyiya bace ga al’umma.”

Kada ku sa mu cikin masu goyon bayan Buari – Kungiyar Musulunci

Kada ku sa mu cikin masu goyon bayan Buari – Kungiyar Musulunci
Source: Twitter

Kungiyar tace “Ku tuna cewa a gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne aka kaddamar da hari akan kungiyar a watan Disamban 2015, inda aka kashe mambobin kungiyar sama da 1000 sannan aka binnesu a rami mai zurfi.

“Maharan (rundunar sojin Najeriya) suka kashe yaran Shugaban kungiyar Sheikh Ibraheem Zakzaky su uku a kan idanunsa, suka harbe shi da matarsa sau da dama sannan suka hana masu kulawar likita, aka kuma tsare su sama da shekaru uku ba bisa doka ba.

KU KARANTA KUMA: Har sai Buhari ya sha kaye hada hadar sanya hannun jari a Najeriya zata farfado - Kwararru

“Kotu ta bayar da umurnin sakin sa amma gwamnati tayi watsi da umurnin kotu sannan ta ci gaba da tsare si duk da raunukan da yake dauke da su, sannan an ana masa samun kulawar likita,” inji sanarwar.

Kungiyar tace idanunta ba a makance suke ba sannan ita ba jahilabace da za ta marawa dan takarar da yayi masu wannan ta’asar baya, sun ce mambobinsu za su yi amfani da kuri’u miliyan takwas da suke dashi cikin hikima.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel