Yanzu Yanzu: Tsohon sakataren tarayya Babachir Lawal bai amsa zargin rashawa da ake masa ba

Yanzu Yanzu: Tsohon sakataren tarayya Babachir Lawal bai amsa zargin rashawa da ake masa ba

- Tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal bai amsa zargin rashawa da ake yi masa ba

- Babacir dai na fuskantar tuhume-tuhume 10 daga hannun hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa

- Ana tuhumar shi tare da wasu mutane biyar kan karkatar da kudaden yankar ciyawa a yankin arewa maso gabas

Tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal bai amsa tuhume-tuhume 10 da hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ke yi a kansa ba.

Lawal da sauran mutane biyar da ake tuhuma a wata babbar kotun Abuja a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairu sun ki amsa laifin tuhumar karkatar da kudaden yankar ciyawa a yankin arewa maso gabas.

Har yanzu ana ci gaba da sauraron shari’an.

Yanzu Yanzu: Tsohon sakataren tarayya Babachir Lawal bai amsa zargin rashawa da ake masa ba

Yanzu Yanzu: Tsohon sakataren tarayya Babachir Lawal bai amsa zargin rashawa da ake masa ba
Source: UGC

A halin da ake ciki, kotu ta bayar da umurnin cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mr Babachir Lawal, zai ci gaba da zama a hannun hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yiwa dukiyar gwamnati zagon kasa (EFCC).

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotun koli tayi watsi da karar APC a jihar Ribas, PDP za taci bulus a zaben 2019

Hakan na nufin cewa hukumar EFCC za ta ci gaba da tsare Mista Babachir Lawal, bayan da kotun a ranar Talata ta ki amincewa da bukatar bayar da belinsa.

Kotun ta sanya ranar Laraba, 13 ga watan Fabreru a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraro shari'ar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel