Rayuka 9 sun salwanta, Mutane 15 sun jikkata yayin aukuwar wani hatsari a jihar Kano

Rayuka 9 sun salwanta, Mutane 15 sun jikkata yayin aukuwar wani hatsari a jihar Kano

Mun samu cewa kimanin rayukan Mutane 9 ne suka salwanta tare da jikkatar Mutane 15 yayin aukuwar wani mummunan hatsarin Mota cikin karamar hukumar Takai da ke jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kakakin kungiyar Direbobin jihar Kano, Nasiru Abu Faragai, shine ya bayar da tabbacin wannan rahoto da cewar hatsarin ya auku ne tsakanin wata Mota kirar Sharon mai lambar BUJ 389 AA- Jigawa da kuma wata Motar kirar Toyota Sienna mai lambar YLA 389 PK-Adamawa.

Rayuka 9 sun salwanta, Mutane 15 sun jikkata yayin aukuwar wani hatsari a jihar Kano

Rayuka 9 sun salwanta, Mutane 15 sun jikkata yayin aukuwar wani hatsari a jihar Kano
Source: Depositphotos

Baya ga tsala gudu da ya wuce ka'ida, hatsarin ya auku ne yayin da daya daga cikin Motocin biyu ke kan hanyar zuwa garin Kano daga birnin Jos, yayin da dayar ke kan hanyarta ta zuwa jihar Adamawa daga Kanon Dabo.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Motocin biyu sun gwabza da juna yayin da Direban daya daga cikin Motocin biyu kirar Toyota ya cika nan take tare da Fasinjoji takwas da ya dauko.

KARANTA KUMA: Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya iso Kotu domin gurfana

An yi gaggawar garzayawa da wadanda suka jikkata zuwa babban Asibitin garin Takai inda a halin yanzu suke ci gaba da samun kyakkyawar kulawa a hannun ma'aikata da kwararru na lafiya.

Mataimakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan tsautsayi a kauyen Madiga da ke karkashin hukumar Takai ta jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel