- Hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana cewa a shekar ta 2018 an samu karin 1.93% na arzikin da muke kirkira da kanmu(GDP)
- A farkon shekara ta 2018 ana samar da gangar mai 1.91m wanda yake kasa da abinda da ake samu a 2017
- GDP a bangaren sha'anin mai ta bunkasa da 1.14% wanda ya kore na shekara ta 2017

Yadda tattalin arzikin Najeriya ya habaka a bara 2018
Source: Facebook
Hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana cewa an samu karin bunkasa a bangaren arzikin da muke kirkira( GDP) da 1.93% a shekara ta 2018.
Bayanin ya nuna cewa an samu 1.6% wanda yake kasa da 3.0% na tsare tsaren da gwamnatin tarraya ta fitar na shekara 2019-2021.
Dadin dadawa rahoton ya nuna cewa tsare tsaren kungiyar bankin duniya da kuma kungiyar harkar kudi na kasa da kasa wanda ya nuna cewa tattalin arziki zai bunkasa da 1.9% a shekara ta 2018.
GA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantun Unity Schools don zabukan makon gobe
A ragowar bangarorin samar da arzikin kuma ya nuna cewa an samu karin bunkasa da 2% wanda ya nunka 0.47% na shekara ta 2017.
A bangaren mai kuma an samu bunkasar da 1.6%,idan aka hade lissafin asalin abinda aka samu a bangaren mai ya kama 1.14 wanda ya kore 4.69% na shekara ta 2017.
A farkon shekara ta 2018 a abinda ake samar wa na gangar mai a kowacce rana yana kaiwa 1.91m wanda yake kasa da 1.94 na shekara ta 2017.
Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa
Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng