An yaba wa hukumar zabe ya INEC kan tunawa da nakasassu masu jefa quri’a

An yaba wa hukumar zabe ya INEC kan tunawa da nakasassu masu jefa quri’a

- Hukumar zabe ta INEC ta samawa nakasassu hanyar kada kuri'ar su cikin sauki

- Hukumar ta sama musu gilasai da kuma takaddun zaben su na daban

- An nemi da su nuna jindadin su ta hanyar fitowa su kada kuri'ar su

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Source: Depositphotos

Mr Samuel Obiefuna coordinator na kungiyar nakasassu yankin jihar Enugu ya bayyana cewa hukumar zabe ta kasa(INEC) ta samarwa da nakasassun hanyar da zasu kada kuri'ar su cikin sauki.

Obiefuna ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da suke gudanarwa da nakasassun bita akan zabe.

Ya bayyana cewa kungiyar ta samar da hanyar sanya nakasassun cikin sha'anin zabe.

Mr George Eze ya mika godiyar sa ga INEC bisa samar da gilasai da takaddar zaben su ta mussaman dan basu damar kada kuri'ar su.

GA WANNAN: Magu: Akwai matsala, yadda kudade ke yawo lokutan zabe, na magudi ne

Yace" Muna godiya bisa ga wannan abu da hukumar zabe tayi mana wanda ya hada harda wayar mana dakai akan yanda zamuyi zaben mu cikin lumana".

Mrs Rose Ezeugwu jami'ar hukumar zabe da aka wakilta dan horar da nakasassun tace" Dan tabbatar da bawa nakasassun dama wajen kada kuri'ar su a zaben shekara ta 2019 hukumar zaben ta samar musu da takaddar tallace tallace ta daban dan nuna musu yanda zasu kada kuri'a.

Ta shawarcesu dasu nuna godiyar su ga hukumar ta hanyar fitowa su kada kuri'ar su a yayin gudanar da zaben.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel