Zaben 16 ga watan Fabreru: Wata kungiyar Igbo ta goyi bayan Atiku

Zaben 16 ga watan Fabreru: Wata kungiyar Igbo ta goyi bayan Atiku

- Kasa da kwanaki hudu da zaben 2019, wata kungiyar ci gaban al'ummar Igbota goyi bayan Atiku Abubakar, da abokin takararsa, Peter Obi

- Kungiyar ta ce babu wata tsiya da gwamnatin Buhari ta tsinanawa shiyyar tasu dama kasar baki daya, da cewar sake zabar APC kamar kunar bakin wake ne

- Kungiyar EPF ta yi Allah-wadai da kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra na cewa Igbo su zauna a gida ba tare da sun fita wajen kad'a kuri'a a wannan zabe ba

Kasa da kwanaki hudu da babban zaben shugaban kasa, wata kungiyar ci gaban al'ummar Igbo, mai suna Estern Peoples Front, ta bayyana mubayi'arta ga dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da abokin takararsa, Peter Obi, tana mai cewa goyawa Atiku baya shine kadai hanyar dorewar Igbo a Nigeria.

Da ya ke jawabi a taron manema labarai a dakin Sports Club, Enugu, shugaban kwamitin kungiyar EPF na kasa, a cikin wata takardar bayan taro da kodinetan kungiyar na kasa, Ken Emechebe ya karanta, ya bayyana cewa babu wata tsiya da gwamnatin Buhari ta tsinanawa shiyyar tasu dama kasar baki daya, yana mai cewa sake zabar gwamnatin APC kamar kunar bakin wake ne.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Gwaman Dickson da matarsa sun isa Heliport domin tarbar Buhari

Zaben 16 ga watan Fabreru: Wata kungiyar Igbo ta goyi bayan Atiku

Zaben 16 ga watan Fabreru: Wata kungiyar Igbo ta goyi bayan Atiku
Source: Facebook

Kungiyar ta ce tana ci gaba da yin riko da mubayi'ar da uwar kungiyar al'ummar Igbo, Ohanaeze Ndigbo suka yiwa Atiku da abokin takararsa Obi, tana mai cewa tana goyon bayan dukkanin ayyukan kungiyar karkashin shugabancin Chief Nnia Nwodo, a matsayin kakakin dukkanin al'ummar Igbo, da cewar duk wanda ya bijirewa Ohanaeze to ya kauce hanyar gaskiya.

Kungiyar EPF ta yi Allah-wadai da umurnin da kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra suka baiwa kabilar Igbo na zaunawa a gida ba tare da sun fita wajen kad'a kuri'a a wannan zabe ba, tana mai cewa hakan gurguwar shawara ce wacce ya zama wajibi kabilar Igbo su yi watsi da ita.

Kungiyar ta ce akwai al'ummar Igbo kusan 26.7m da suka yi rijistar zabe a fadin kasar, kuma kungiyar EPF na ci gaba da gangamin wayar da kan al'ummar Igbo akalla 16m akan fa'idojin zaben Atiku Abubakar a ranar 16 ga watan Fabreru.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel