Yanzu-yanzu: Kotun koli tayi watsi da karar APC a jihar Ribas, PDP za taci bulus a zaben 2019

Yanzu-yanzu: Kotun koli tayi watsi da karar APC a jihar Ribas, PDP za taci bulus a zaben 2019

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da jam''iyyar All Progressives Congress APC ta shigar na kalubalantan shari'ar babban kotun jihar Ribas wacce ta haramtawa jam'iyyar gudanar da zaben fidda gwani a shekarar 2018.

Wannan na nuna cewa jam'iyyar APC ba za tayi musharaka a zaben 2019 ba a dukkan kujerun takara a jihar Ribas.

Mun kawo muku a baya cewa Yunkurin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wajen musharaka cikin zaben 2019 a jihar Rivers ya samu cibaya yayinda kotun daukaka kara ta tabbatar da shari'ar babban kotun jihar na watsi da dukkan zabukan fidda gwanin da jam'iyyar ta gudanar.

Kotun daukaka karan dake zaune a Fatakwal ta yi watsi da karar da jam'iyyar APC ta shigar na kalubalantar shari'ar Jastis Chiwendu Nworgu wanda yace za'a yi zaben jihar ba tare da jam'iyyar APC ba.

Bayan sauraron jawabin lauyoyin bangarorin biyu, Jastis C.N Uwa ta bayyana cewa shari'ar kotun jihar Ribas da suka zo daukakawa, harka ne da ta shafi zaben fidda gwani kuma ya kamata a ce an daukaka karan cikin kwanaki 60.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel