Har sai Buhari ya sha kaye hada hadar sanya hannun jari a Najeriya zata farfado - Kwararru

Har sai Buhari ya sha kaye hada hadar sanya hannun jari a Najeriya zata farfado - Kwararru

Rahotanni sun kawo cewa hada hadar sanya hannun jari Najeriya na iya habbaka idan har Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi zaben karshen makon nan mai zuwa, kamar yadda Citigroup tayi hasashe.

An tattaro cewa tun bayan hawan shugaba Buhari mulki a watan Mayun 2015, darajar hannun jarin kasar ya fadi warwas a duniya ta fannin dala.

Wasu daga cikin masu zuba jari a kasashen waje za su fi son gwamnati karkashin babban abokin adawar Buhari, dan kasuwa kuma tsohon sugaban kasa Atiku Abubakar.

Har sai Buhari ya sha kaye hada hadar sanya hannun jari a Najeriya zata farfado - Kwararru

Har sai Buhari ya sha kaye hada hadar sanya hannun jari a Najeriya zata farfado - Kwararru
Source: Depositphotos

Sai dai yayinda Atiku ya sha alwashin siyar da wasu kadarorin kasar da kuma daga darajar naira, mutane da dama na kokwanto akan matsayarsa game da rashawa.

KU KARANTA KUMA: Rikicin SDP ya dauki sabon salo yayinda bangaren Gana suka mara wa Atiku baya

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shugaban yakin neman zaben Atiku Abubakar da kuma Peter Obi na PDP a zaben 2019 a jihar Anambra, Oseloka Obaze, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya riga ya fadi zaben 2019 da za ayi.

A Ranar Laraban nan ne Mista Oseloka Obaze ya fito ya bayyana cewa za ayi waje da gwamnatin shugaba Buhari a zaben da za ayi a Ranar 16 ga watan Fubrairu. Obaze yace yanzu jira kurum ake yi Atiku ya zama shugaban kasa.

Obaze wanda yayi takarar gwamnan jihar Anambra a zaben 2017, ya bayyana cewa fiye da kashi 90% na mutanen Najeriya sun gaji da gwamnatin nan mai-ci ta shugaba Buhari don haka za su zabi ‘dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel