Yanzu yanzu: Gwaman Dickson da matarsa sun isa Heliport domin tarbar Buhari

Yanzu yanzu: Gwaman Dickson da matarsa sun isa Heliport domin tarbar Buhari

Rahotannin da Legit.ng ke samu a yanzu na nuni da cewa gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson na zaman jiran isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a filin sauka da tashin jirage na King Alfred Diete Spiff Heliport, da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Buhari zai kai ziyara jihar ne, a ci gaba da kaddamar da yakin zabensa. Ana sa ran shugaban kasar zai dira dira da misalin kafe 11 na safe. A cikin tawagar gwamnan, akwai matarsa, da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin jihar Bayelsa.

Uwar gidan gwamnan jihar, Dr Rachael Dickson ta bi sahun mijin nata, Seriake Dickson wajen jiran isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a filin saukar jiragen na Heliport, domin kaddamar daq yakin zaben APC a jihar

A na sa ran shugaban kasa Buhari zai kaddamar da yakin zabensa a filin wasanni na Oxbow Lake, Bayelsa.

Cikakken labarin yana zuwa..

KARANTA WANNAN: Ku rubuta ku aje: Yakin zaben PDP a Kano 'yar manuniya ce ta faduwar APC - Mr LA

Yanzu yanzu: Gwaman Dickson da matarsa sun isa Heliport domin tarbar Buhari

Yanzu yanzu: Gwaman Dickson da matarsa sun isa Heliport domin tarbar Buhari
Source: Depositphotos

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel