Ba kamar wa'e ba, ni ba zanyi katsalandan a ayyukan Majalisu da na Sharia ba

Ba kamar wa'e ba, ni ba zanyi katsalandan a ayyukan Majalisu da na Sharia ba

- Atiku yaje Fatakwal

- Yayi alkawarin sauya tsari ba irin na Buhari ba

- Shugaba Buhari ya sauke alkalin Alkalai

Ba kamar wa'e ba, ni ba zanyi katsalandan a ayyukan Majalisu da na Sharia ba

Ba kamar wa'e ba, ni ba zanyi katsalandan a ayyukan Majalisu da na Sharia ba
Source: Instagram

Mai jiran jama'a su zabe shi a makon nan, ya zame musu shugaban kasa, Atiku Abubakar na PDP, ya alkawartawa 'yan Najeriya cewa, ba zai yi katsalandan a harkokin bangarorin gwamnati guda biyu da basu karkashin zababbu ba.

Bangarorin sune, na Sharia da na majalisu, wadanda suka ga katsalandan daga bangaren shugaban kasa musamman kan banbancin siyasa da na zargin cin hanci da rashawa.

Gwamnatin Tarayya, tayi kokarin sauke shugabannin Majalisu, lamari da ya kai su har suka nuna basu son shugaban kasar ya zarce, suka koma PDP.

GA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantun Unity Schools don zabukan makon gobe

Atiku Abubakar, a birnin Fatakwal, a zagayen da yake na neman yarjewar 'yan Najeriya, yayi alkawarin ba zai sauke Alkalain Alkalai ba koda ana zarginsa da cin hanci, zai mika wa majalisin sharia na koli su duba batun, kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Atiku kuma, ya zargi shugaba Buhari da raba kan 'yan Najeriya, da ma ingiza jama'a su tayar da hankali.

aura kwanaki hudu dai a gama kamfe na shiga manyan zabukan 2019, kuma ana sa rai tsakanin Atiku da Buhari ne za'a fafata.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel