Ku rubuta ku aje: Yakin zaben PDP a Kano 'yar manuniya ce ta faduwar APC - Mr LA

Ku rubuta ku aje: Yakin zaben PDP a Kano 'yar manuniya ce ta faduwar APC - Mr LA

- Mr LA ya bayyana irin tarbar da al'ummar jihar Kano suka yi wa Atiku Abubakar, 'yar manunuya ce akan faduwar jam'iyyar APC da tan takararta Buhari a zabe mai zuwa

- Ya ce APC ta san ba zata iya ci gaba da kasancewa akan mulki ba la'akari da irin alkawuran da ta daukarwa 'yan Nigeria a 2015 kuma ta gaza cika su

- Mr LA ya kuma ce Buhari ya yaudari 'yan Nigeria da alkawuran karya, ya gaza kawo karshen matsalolin tsaro, yunwa, talauci, gine gine da kuma uwa uba rashin aikin yi

Dan takarar sanatan mazabar Kaduna ta tsakiya karkashin jam'iyyar PDP, Lawal Adamu Usman (Mr LA), ya bayyana irin tarbar da al'ummar jihar Kano suka yi wa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, Atiku Abubakar, 'yar manunuya ce akan faduwar jam'iyyar APC da tan takararta Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan watsa labarai na Mr. LA, Abdul-Azeez Suleiman, ya bayyana irin nasarorin da APC ke samu a fadin kasar a matsayin alama karara ta zuwan karshen mulkin APC a kasar.

KARANTA WANNAN: Yakin zabe: Mun tuntubi masu kada kuri'a miliyan 20 ta wayar salula da rokon su zabe mu - APC

Ku rubuta ku aje: Yakin zaben PDP a Kano 'yar manuniya ce ta faduwar APC - Mr LA

Ku rubuta ku aje: Yakin zaben PDP a Kano 'yar manuniya ce ta faduwar APC - Mr LA
Source: Facebook

"Gaba daya 'yan takara sun san cewa babban jigon samun nasara a zabe shine irin alkawuran da ya daukarwa jama'arsa. Amma a gaskiyar magana, babban jigon samun nasara a siyasa shine cika wannan alkawarin da dan takara ya dauka," a cewar sanarwar.

"APC ta san ba zata iya ci gaba da kasancewa akan mulki ba la'akari da irin alkawuran da ta daukarwa 'yan Nigeria a 2015 kuma ta gaza cika su, masu yakin zaben APC sun yi alkawuran warkar da 'yan kasar, da magance tsaro, yaki da jahilci, rashin aikin yi da kuma talauci

"Sai dai abun takaicin shinje yadda a tsawon kusan shekaru hudu na gwamnatinta, APC ta gaza cika wadannan alkawuran da ta dauka. Buhari ya yaudari 'yan Nigeria da alkawuran karya, ya gaza kawo karshen matsalolin tsaro, yunwa, talauci, gine gine da kuma uwa uba rashin aikin yi da tabarbarewar tattalin arzikin kasar" a cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel