Kididdigar jin ra'ayi: Shugaba PMB ne zai lashe zaben makon nan da Najeriya zata yi

Kididdigar jin ra'ayi: Shugaba PMB ne zai lashe zaben makon nan da Najeriya zata yi

- Kungiyoyi har biyu sunyi hasashen shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma kujerar shi

- Shugaban ya kasance mai magoya baya a yankunan arewa da kudu maso yamma, wadanda ke da mafi yawan masu kada kuri'u

- Rashin isashen kudin kamfen da rabuwar kan gwamnonin cikin gida shine babban kalubale ga PDP

Kididdigar jin ra'ayi: Shugaba PMB ne zai lashe zaben makon nan da Najeriya zata yi

Kididdigar jin ra'ayi: Shugaba PMB ne zai lashe zaben makon nan da Najeriya zata yi
Source: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi nasara a zaben asabar mai zuwa kamar yanda kungiyoyi biyu na bincike akan zabe NOI da British Business group suka bayyana.

Sun gano cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sune jiga jigan yan takarar da zasu kara, sauran kuwa duk yan bin yarima ne asha kida.

Binciken nasu bai ci karo da binciken Eurasia group dake New York ba, kungiyar da tayi hasashen cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi nasara da kashi 60 ne.

NOI wacce Anap Foundation ta kaddamar da jagorancin Atedo Peterside, ta gano cewa tushen goyon bayan Buhari ya dogara ne da abubuwa 6. Sune: Cigaba, yaki da rashawa, nagarta, inganta tsaro, taimakon talakawa da kuma zabin mutane.

Su kuma masu son Atiku suna yi ne saboda kara habaka tattalin arziki, shugabanci na gari, zabin su, tarihin siyasar shi da gyare gyare.

Binciken ya nuna rashin damuwar masu zabe a kudu maso yamma da kudu maso gabas, ba kamar arewa maso yamma,arewa maso gabas da arewa ta tsakiya ba.

Kungiyar ta gano cewa ba abin mamaki bane don masu zabe sun nuna rashin damuwar su akan zabe mai gabatowa gani da cewa duk yan takarar musulmai ne kuma basu da hadi da kudun.

GA WANNAN: Lauyan Shagari ya kwashe wa 'yan siyasar zamani albarka, ya rage daya tal

"Cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari shi zai jagoranci yawan kuri'u saboda kaso 1 bisa uku ne na fadin kasar nan basu goyon bayan shi. Atiku Abubakar kuwa an barshi a baya."

An jaddada: "Buhari ne zai yi nasar, Buhari ne ke da arewa da kudu maso yamma, yankunan da suka fi yawan masu kada kuri'a."

Ita kuna kungiyar kasuwanci ta Birtaniya tace goyon bayan shugaba Buhari na da tsushe ne a yankunan arewa da kudu maso yamma wanda duk kokarin yan adawa bazasu taba iya hanawa ba.

Kungiyar tace: "Buhari na da magoya baya a arewa da kudu maso yamma, yankunan da suka fi yawan masu kada kuri'u. PDP zata yi ta kokarin samo magoya baya har da ma inda tasan bata dasu amma zata fuskanci damuwa ta rashin kudin yakin neman zabe da kuma rabuwar kan cikin gida tsakanin gwamnonin ta."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel