Yakin zabe: Mun tuntubi masu kada kuri'a miliyan 20 ta wayar salula da rokon su zabe mu - APC

Yakin zabe: Mun tuntubi masu kada kuri'a miliyan 20 ta wayar salula da rokon su zabe mu - APC

- Jam'iyyar APC ta ce ta samu nasarar tuntubar masu kada kuri'a miliyan ashirin a fadin Nigeria ta hanyar kiransu kai tsaye ta wayar salula

- Daraktan ayyukan kai tsaye na yakin zaben jam'iyyar APC, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja

- Ribadu ya bayyana cewa kusan matasa 67,000 da ke aiki karkashin sashen da yake kula da shi suna yi ne kyauta ba domin a biya su ba sai don ci gaban kasar

Jam'iyyar APC ta ce ta samu nasarar tuntubar masu kada kuri'a miliyan ashirin a fadin Nigeria ta hanyar kiransu kai tsaye ta wayar salula, a ci gaba da yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, musamman a yanzu da ya rage saura kwanaki hudu babban zabe na kasar.

Daraktan ayyukan kai tsaye na yakin zaben jam'iyyar APC, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja.

Ribadu wanda ya yi jawabi a sakatariyar sashen ayyukan kai tsaye na kungiyar yakin zaben, ya ce shi da tawagarsa sun kaddamar da yakin zaben shugaban kasar a lunguna da sakunan kasar, walau ta hanyar tuntuba kai tsaye ko ta hanyar wayar salula, da kuma kafofin sadarwa na zamani.

KARANTA WANNAN: Salon mulkin Buhari ya dace da Nigeria da ma Afrika baki daya - Gwamna Masari

Yakin zabe: Mun tuntubi masu kada kuri'a miliyan 20 ta wayar salula da rokon su zabe mu - APC

Yakin zabe: Mun tuntubi masu kada kuri'a miliyan 20 ta wayar salula da rokon su zabe mu - APC
Source: Twitter

Ya ce an kasa sashen zuwa kwamitoci ukku domin gudanar da yakin zaben. Yana mai cewa kwamitocin sun hada da: Kwamitin tuntubar masu kada kuri'a kai tsaye ta kiran wayar tarho, kwamitin yakin zaben gida-gida da kuma kwamitin yakin zabe ta kafar sadarwa ta zamani.

Ya ce sun kasa sashen ne zuwa kwamitoci ukku domin baiwa kowanne kwamiti damar tuntubar akalla kashi daya cikin kashi hamsin na masu kad'a kuri'u a fadin kasar.

Tsohon shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da kuma yiwa dukiyar gwamnati zagon kasa EFCC ya ce sashen da ke karkashinsa na gudanar da yakin zabenne ta hanyar mutane masu sa kai da ke yi ba domin a biya su ba, sai domin ci gaban kasar.

Ya bayyana cewa kusan matasa 67,000 da ke aiki karkashin sashen da yake kula da shi musamman a kwamitin yakin zaben gida-gida da kuma na tuntuba ta wayar salula suna yi ne kyauta ba domin a biya su ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel