Rikicin SDP ya dauki sabon salo yayinda bangaren Gana suka mara wa Atiku baya

Rikicin SDP ya dauki sabon salo yayinda bangaren Gana suka mara wa Atiku baya

- Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a ranar Litinin, 11 ga watan Fabarairu ya dauki sabon salo

- Bangaren jam’iyyar ta kuma tsayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na Shugaban kasa

- Tace ta zabi Atiku ne saboda kudirinsa na son sake fasalin lamuran kasar

Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a ranar Litinin, 11 ga watan Fabarairu ya dauki sabon salo yayinda wani bangare na jam’iyyar masu biyayya ga Farfesa Jerry Gana suka sanar da dakatar da mukaddasin shugabanta na kasa Farfesa Tunde Adeniran da Alhaji Shehu Gabam, a matsayin sakatare da mataimakin dan takarar Shugaban kasa.

Ta kuma amince da nadin Mista Supo Sonibare tsoon mataimakin Shugaban jam’iyyar a matsayin mukaddashin Shugaban jam’iyyar na kasa.

Rikicin SDP ya dauki sabon salo yayinda bangaren Gana suka mara wa Atiku baya

Rikicin SDP ya dauki sabon salo yayinda bangaren Gana suka mara wa Atiku baya
Source: Depositphotos

Shugabannin jam’iyyar, a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya a ranar Litinin bangaren jam’iyyar ta kuma tsayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na Shugaban kasa a zabe mai zuwa yayinda dan takararta yayi adawa da zabar dan takarar APC, Muhammadu Buhari da jam’iyyar tayi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: INEC ta fitar da samfurin kuri'u da akwatunan zabe, hotuna

A cewar wata sanarwa daga sabon sakataren jam’iyyar na bangaren Gana, Adakole Ijogi, yace jam’iyyar ta zabi Atiku ne saboda kudirinsa na son sake fasalin lamuran kasar.

A halin da ake ciki, mun ji cewa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake jaddada matsayar sa ta tabbatar da sauya fasalin kasar nan ta Najeriya tare da yi mata garambawul yayin nasarar sa zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

A jiya Litinin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar da tabbacin sa na sauya fasalin Najeriya a matsayin aiki na farko da zai gudanar da zarar ya karbi mulkin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel