Salon mulkin Buhari ya dace da Nigeria da ma Afrika baki daya - Gwamna Masari

Salon mulkin Buhari ya dace da Nigeria da ma Afrika baki daya - Gwamna Masari

- Gwamna Masari, ya ce PDP na son ta dawowa mulki ne kawai domin lalata duk wani ci gaba da shugaban kasa Buhari ya kawowa kasar

- Ya kuma jaddada cewa a mulkin PDP, an samu tabarbarewar tsaro, sace dukiyar kasa da kuma lalacewar duk wasu ma'adanai na kasar

- Masari ya ce irin salon shugabancin da Buhari ya ke yi a Nigeria shine yafi dacewa da kasar domin irinshi ne kasashen Afrike ke muradin samu

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi fatali da yunkurin babbar jam'iyyar adawa ta PDP na sake dawowa shugabancin Nigeria, yana mai cewa PDP na son ta dawo mulki ne kawai domin lalata duk wani ci gaba da shugaban kasa Buhari ya kawowa kasar tare da jan koma baya ga dukkanin ayyukan da ya tsara domin amfanar masu zuwa kasar a karnoni na gaba.

Da ya ke karbar bakuncin mataimakin shugaban APC na kasa reshen shiyyar Arewa da kuma jagoran kungiyar goyon bayan tazarcen Buhari, Sanata Lawal Shuaibu, gidan gwamnatin Katsina a jiya Litin, Masari ya yi ikirarin cewa baiwa PDP wata damar zai sake mayar da kasar a halin da ta tsinci kanta na tsawon shekaru 16 na mulkinta.

"Kamar dai yadda muke 'yan Adam, muna da yawan mantuwa, inba domin hakan ba ai da kowa zai hakikance cewa tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari shine ya fi dacewa da Nigeria, kai har ma da kasashen Afrika, irin salon shugabancinsa ake so a Afrika gaba daya."

KARANTA WANNAN: Ta leko ta koma: Tsohon shugaban kasar Amurka ya soke ziyarar da zai kawo Nigeria

Salon mulkin Buhari ya dace da Nigeria da ma Afrika baki daya - Gwamna Masari

Salon mulkin Buhari ya dace da Nigeria da ma Afrika baki daya - Gwamna Masari
Source: Facebook

Masari ya ce akwai wasu da basa son ci gaban kasar, wadanda ke a cikin shirin samun wata 'yar karamar dama domin sake tafka uba uban almundahana da almubazzaranci da dukiyar kasar, kasancewar ba su da wani salon shugabanci na adalci ko gaskiya.

Ya kuma jaddada cewa a mulkin PDP, an samu tabarbarewar tsaro, sace dukiyar kasa da kuma lalacewar duk wasu ma'adanai na kasar, yana mai cewa halin da kasar ta ke ciki a yanzu, ya zarce wanda ta ke a baya nesa ba kusa ba.

"Irin namijin kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke yi na ganin ya kai kasar zuwa mataki na gaba abun a yaba ne kuma a kara bashi kwarin guiwa, amma duk wanda ya ke tunanin akasin hakan lallai bai san kalubalan da ke tattare da juyawa Buhari baya ba.

"Muna sane da irin yadda Buhari ya kawo karshen matsalolin tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas, musamman jihohin Borno, Yobe da Taraba, kowa ya san irin kuncin rayuwar ta'addanci da suka shiga a baya har zuwa 2015."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel