Masu garkuwa da mutane sun kashe Malamin jami’a, sun yi awon gaba da guda 2

Masu garkuwa da mutane sun kashe Malamin jami’a, sun yi awon gaba da guda 2

Wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun halaka wani Malami dake koyarwa a wata jami’a mai zaman kanta, BOWEN dake garin Iwo cikin jahar Osun a ranar Litinin, 11 ga watan Feburairu.

Sai dai yan bindigan basu tsaya nan ba, sai da suka yi awon gaba da wasu Malaman jami’ar ta BOWEN su biyu da nufin yin garkuwa dasu har sai an biyasu makudan kudade a matsayin kudaden fansa kafin su sakesu, kamar yadda suka saba.

KU KARANTA: Akwai matsala: Akwai marasa aikin yi guda 4,000,000 a tsakanin jahar Kano da Jigawa

Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar Osun, DSP Folashade Odoro ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace tuni kwamishinan Yansandan jahar ya tura wasu jami’an Yansanda hanyar Iwo zuwa Osogbo, inda lamarin ya faru da nufin gano inda Malaman suke.

“Eh, an yi garkuwa da mutane guda biyu, amma tuni mun aika da Yansandanmu zuwa dazukan yankin hanyar Iwo zuwa Osogbo da nufin gudanar da bincike a yankin domin ceto wadanda aka yi garkuwa dasu tare da kama miyagun mutanen.” Inji ta.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yan bindigan sun dade suna bibiyan Malaman tun daga lokacin da suka fito daga makarantar bayan sun tashi daga aiki, sai dai yace akwai wani Malami guda da yayi kokarin tserewa, amma yan bindigan suka bude masa wuta.

Idan za’a iya tunawa a shekarar da ta gabata ma masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani limamin Cocin Methodist da jama’ansa a wannan hanya ta Iwo zuwa Osogbo, inda sai da aka biya naira miliyan 3 suka sakosu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel