Da duminsa: EFCC ta cafke Babachir Lawal, za ta gurfanar da shi yau kan zargi handame N544.1m

Da duminsa: EFCC ta cafke Babachir Lawal, za ta gurfanar da shi yau kan zargi handame N544.1m

- Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnatin tarayya (SGF) Babachir Lawal. A yau ne hukumar EFCC ta shirya gurfanar da Lawal gaban kotu

- Hukumar tana zargin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da aikata laifuka 10 da suka shafi hada baki tare da sama da fadi da kudaden gwamnati

- Gaba daya wadanda ake zargin za su gurfana ne gaban babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, bisa zarginsu da sama da fadi da N544,119,9225.36m

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da kuma masu yiwa dukiyar gwamnati zagon kasa (EFCC) ta cafke tsohon gwamnatin tarayya (SGF) Babachir Lawal. A yau ne hukumar EFCC ta shirya gurfanar da Lawal gaban kotu.

Hukumar tana zargin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da aikata laifuka 10 da suka shafi hada baki tare da sama da fadi da kudaden gwamnati, ta hanyar bayar da kwangilar bogi. Hukumar tana tuhumar Lawal ne tare da wasu mutane ukkuu da kamfanoni biyu.

Mutanen da kamfanonin da ake tuhumarsu tare da Lawal, sun hada da: Hamidu David Lawal; Sulaiman Abubakar; Apeh John Monday; kamfanin Rholavision Engineering Limited da kuma kamfanin Josmon Technologies Limited.

KARANTA WANNAN: Kar ku biyewa zantukan 'yan adawa, ku zabeni a Maris - El-Rufai ya roki Kirista

Da duminsa: EFCC ta cafke Babachir Lawal, za ta gurfanar da shi yau kan zargi handame N544.1m

Da duminsa: EFCC ta cafke Babachir Lawal, za ta gurfanar da shi yau kan zargi handame N544.1m
Source: UGC

Gaba daya wadanda ake zargin za su gurfana ne gaban babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, bisa zarginsu da sama da fadi da N544,119,9225.36m, na kudin kwangilar cire wata ciyawa da kuma saukaka noman rani.

Amma gabananin gurfanar da su, a jiya Litinin, hukumar EFCC ta cafke tsohon sakataren gwamnatin tarayyar tare da garkame shi a ofishinta.

Wata majiya ta ce: "Mun cafke Babachir Lawal tare da tsare shi a ofishinmu tare da wasu da ake zargi a shirye shiryen gurfanar da su a ranar Talata."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel