Sauya fasalin kasa zan fara aiwatar wa idan na hau Kujerar mulki - Atiku

Sauya fasalin kasa zan fara aiwatar wa idan na hau Kujerar mulki - Atiku

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake jaddada matsayar sa ta tabbatar da sauya fasalin kasar nan ta Najeriya tare da yi mata garambawul yayin nasarar sa zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

A jiya Litinin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar da tabbacin sa na sauya fasalin Najeriya a matsayin aiki na farko da zai gudanar da zarar ya karbi mulkin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu.

Atiku da jiga-jigan PDP yayin yakin zaben sa a jihar Ribas

Atiku da jiga-jigan PDP yayin yakin zaben sa a jihar Ribas
Source: Twitter

Atiku ya sake bayar da wannan tabbaci ne a jiya Litinin cikin jawaban sa ga magoya baya yayin taron sa na yakin zabe da ya gudanar a harabar filin wasanni na Adokiye Amiesimaka da ke birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Wazirin Adamawa tare da abokin takarar sa, Peter Obi da kuma sauran jiga-jigai na jam'iyyar PDP, sun sha alwashin riko da doka tare da yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan da'a a kowane yanayi yayin da suke rike da akalar jagorancin kasar nan.

KARANTA KUMA: Kotu ta aika wa Oshiomhole sammaci kan rikicin APC a jihar Imo

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma sha alwashin dawo da martabar birnin Fatakwal muddin ya yi nasara a babban zabe da za a gudanar a ranar Asabar mai gabatowa.

Cikin jawaban su duba da yadda gwamnatin jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi riko na sakainar kashi wajen tafiyar da al'amurran kasar nan, Atiku da abokin takarar sa sun sha alwashin dawo da duk wata martaba ta inganci a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel