Sai mun karbe Jihar Kwara daga wajen Bukola Saraki – Bola Tinubu

Sai mun karbe Jihar Kwara daga wajen Bukola Saraki – Bola Tinubu

- Jiga-jigan APC sun dura Jihar Kwara inda su ke sa ran tika Saraki da kasa

- Asiwaju Bola Tinubu yace APC ta shirya karbe Jihar Kwara a zaben bana

- Shugaban Jam’iyyar APC yace Bukola Saraki ya hana Jihar Kwara sakat

Sai mun karbe Jihar Kwara daga wajen Bukola Saraki – Bola Tinubu

Oshiomhole yace Bukola Saraki ya hana Jihar samun cigaba
Source: UGC

Mun samu labari cewa, Asiwaju Bola Tinubu, yayi kira ga Mabiyan sa da su yi kokarin ganin sun zabi APC a zaben da za ayi mako mai zuwa domin ganin sun fita daga kangin da Bukola Saraki ya jefa jihar na tsawon lokaci.

Babban jigon jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bayyana wannan ne a lokacin da jirgin yakin zaben Buhari ya shiga jihar Kwara jiya Ranar Litinin. Bola Tinubu yace jam’iyyar su ta APC ta shirya karbe mulki a jihar Kwara.

KU KARANTA: Don na hana Tinubu zama Mataimakin Buhari shiyasa yake babatu - Saraki

Tsohon gwamnan na Legas yayi jawabin sa ne da harshen yarbanci wajen kamfe din inda yace Bukola Saraki ya dade yana barnatar da dukiyar al’umman jihar Kwara. Tinubu yace APC za ta ceci jihar daga wannan bauta da aka jefa su.

Asiwaju Tinubu yace ba kowa bane yake facaka da dukiyar mutanen Kwara illa Bukola Saraki don haka ya nemi jama’a su nemawa kan su mafita ta hanyar zaben ‘dan takarar APC na gwamna watau Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq.

KU KARANTA: Atiku ya sake hada zugar jama'a a Ribas bayan gangamin Kano

Tinubu yake cewa APC ba ta da matsala da mahaifin shugaban majalisar dattawan watau Marigayi Olusola Saraki inda har ya roka masa Aljanna. Cikin wadanda su kayi wa Tinubu rakiya har da jagorar APC a jihar, Gbemisola Saraki.

A wajen taron da APC ta shirya, shugaban Jam’iyyar, Adams Oshiomhole ya zargi Saraki da nakasa jihar inda yace tsohon gwamnan ne ya hana Jihar cigaba domin kuwa har gobe shi ne yake juya gwamna mai-ci kamar wani yaron sa.

APC dai ta shirya kamfe a jihar Kwara inda shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma manyan jam’iyyar irin su Bisi Akande da Sanata Abdullahi Adamu, da kuma Adams Oshiomhole su ka halarta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel