2019: Saraki ya maidawa Tinubu raddi bayan APC sun yi kamfe a Kwara

2019: Saraki ya maidawa Tinubu raddi bayan APC sun yi kamfe a Kwara

- Bukola Saraki ya bayyana abin da ya sa har gobe Bola Tinubu yake jin haushin sa

- Saraki yace yana cikin wadanda su ka hana Bola Tinubu zama Mataimakin Buhari

- Shugaban Majalisar Dattawan yace wannan ya sa Tinubu yake ta sukar sa har gobe

2019: Saraki ya maidawa Tinubu raddi bayan APC sun yi kamfe a Kwara

Saraki yace su su ka hana Tinubu ya zama Mataimakin Shugaban kasa
Source: UGC

Mun samu labari cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya bayyana cewa yana cikin wadanda su kayi kokarin ganin an hana Bola Ahmed Tinubu tikitin mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC a shekarar 2015.

Bukola Saraki yace wannan abu ne ya sa har yanzu babban jigon na APC ya rike sa a ran sa tun wancan lokaci. Saraki yana maida martani ne bayan sukar da ya sha a hannun Asiwaju Bola Tinubu wajen kamfen din APC jiya a jihar Kwara.

KU KARANTA: Buhari ya nemi Jama’a su zabi duk wanda su ke so a zaben 2019

Saraki ya fitar da wannan jawabi te bakin wani hadimin sa, Yusuph Olaniyonu. Sanatan yace bai goyi bayan a bar Tinubu yayi takara bane saboda ganin cewa shi ma Musulmi irin Muhammadu Buhari wanda zai rikewa APC tuta a lokacin.

Shugaban majalisar tarayyar yace kishin kasa ya hana ya amince a bar Musulmai biyu su yi takara a APC a 2015 don haka har yau Tinubu yake bakin cikin yadda shi Saraki ya hana sa samun kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Tinubu dai yayi kira ga jama’an Kwara su raba kan su daga takunkumin da Bukola Saraki ya kakaba masu ta hanyar zaben APC wannan karo. Saraki yayi wuf yayi raddi inda yace bakin cikin hana sa takara ne ya sa shi wannan magana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel