Dattawan Arewa ba su goyi bayan Atiku ba - Junaidu

Dattawan Arewa ba su goyi bayan Atiku ba - Junaidu

- Jigo a kungiyar dattawan Arewa, Dr Junaid Mohammed ya ce kungiyar ba ta zabi Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugabancin kasa da zata marawa baya ba

- Dr Mohammed ya ce sanarwar marabawa Atiku baya ra'ayi ne kawai na wasu tsirarun 'yan kungiyar karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi

- Tsohon na majalisar ya ce kungiyar ta taba gayyatan 'yan takarar shugabancin kasa na PDP a baya amma bata cimma matsayar goyon bayan kowa ba a cikinsu

Dan majalisa na jamhuriya ta biyu kuma fitaccen mamba na kungiyar dattawan Arewa, NEF, Dr Junaid Mohammed ya ce kungiyar ba ta zabi dan takarar shugabancinkasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a matsayin wanda za ta marawa baya ba.

A cewar Mohammed, wasu tsiraru cikin 'yan kungiyar ne karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi suke goyon bayan Atiku.

DUBA WANNAN: Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da ba su taba sauya sheka ba

Dattawan Arewa ba su goyi bayan Atiku ba - Junaidu

Dattawan Arewa ba su goyi bayan Atiku ba - Junaidu
Source: Depositphotos

A makon da ta gabata, shugabani da wasu mambobin yankunan siyasar kasar nan sun sanar da goyon bayansu ga takarar Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a zaben ranar 16 ga watan Fabarairun 2019.

Wannan ya biyo bayan wani taro ne da shugabanin suka gudanar a Sheraton Hotel da ke Abuja inda shugabanin wasu kungiyoyi da suka hada da Ohaneze Ndigbo, Pan-Niger Delta, Middle Belt Forum da wani bangare na Afenifere suka hade da NEF suka sanar da cewa Atiku ne dan takarar da za su zaba.

Sai dai a hirar da The Nation tayi da Mohammed a jiya Litinin, ya ce NEF ba ta tsayar da wani dan takarar da zata marawa baya ba zaben shugaban kasa na wannan shekarar.

"Babu wani lokaci da muka zauna muka tattauna goyon bayan wani dan takarar shugabancin kasa a NEF. Abinda aka sanar ra'ayi ne kawai na Farfesa Ango Abdullahi. Duk lamarin karya ce tsantsagwaranta," inji shi.

Da ya ke bayani akan abinda ya haifar da rikicin tun farko, ya ce kungiyar ta gayyaci yan takarar shugabancin kasa na PDP domin tattaunawa da su amma ba a cimma matsayar goyon bayan kowa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel