Akwai matsala: Akwai marasa aikin yi guda 4,000,000 a tsakanin jahar Kano da Jigawa

Akwai matsala: Akwai marasa aikin yi guda 4,000,000 a tsakanin jahar Kano da Jigawa

Zaman banza, zaman kashe wando da kuma rashin aikin yi na daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta a Najeriya a yau, musamman ma a yankin Arewacin Najeriya, yankin da yafi sauran yankunan kasar yawan al’umma.

Wani malami a jami’ar Bayero, kuma shugaban kwalejin horas da ilimin kasuwanci ta Dangote dake jami’ar, Farfesa Murtala Sagagi ya bayyana cewa akwai matasa marasa aikin yi guda miliyan hudu (4,000,000) a tsakanin jahar Kano da jahar Jigawa.

KU KARANTA: Matukar Buhari ya fadi zaben 2019, APC ta mutu murus – Shehu Sani

Farfesa Sagagi ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da yayi da dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a daren Lahadi, 10 ga watan Feburairu bayan kammala yakin neman zabensa daya gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake garin Kano.

A jawabinsa, Sagagi ya bayyana ma Atiku Abubakar cewa a jahar Kano kadai akwai marasa aikin yi da yawansu ya kai miliyan uku da dubu dari uku, 3.3m, yayin da jahar Jigawa ke da adadin marasa aikin yi da suka kai dubu dari bakwai (700,000).

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Farfesan ya bayyana cewa ya samu wadannan alkalumma ne daga wani kwamitin bincike da yayi aiki da ita a kwanakin baya, har ma ya kara da cewa a jahar Kaduna kuwa akwai mutanen dake bukatar aikin yi da suka kai miliyan daya da dubu dari uku, 1.3m.

Sagagi ya bayyana damuwarsa da miliyoyin matasan Arewacin Najeriya da badu da aikin yi, wanda hakan yasa yayi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa dasu baiwa samar da aikin yi ga matasa muhimmanci ta hanyar tayar da kamfanonin da suka durkushe.

Farfesan ya cigaba da cewa a jahar Kano kadai akwai kamfanoni guda dubu biyar da dari biyar, amma a yanzu guda dari hudu ne kawai suke aiki, sa’annan ya danganta matsalar rashin cigaba a Arewa ga rashin takamaimen hanyar dabbaka tsare tsaren gwamnati.

Daga karshe a nasa jawabi, Atiku Abubakar ya tabbatar ma mahalarta taron cewa idan har ya samu darewa mukamin shugaban kasar Najeriya a 2019 zai magance matsalar rashin aiki ta hanyar tallafa ma matsakaita da kananan masana’antu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel